Home Back

Rikicin Iran da Isra'ila ya nuna yadda ƙasashen suka kasa fahimtar juna

bbc.com 2024/5/2

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Jirgin yaƙin Isra'ila ƙirar Amurka
Bayanan hoto, Iran ta ce harin da Isra'ila ta kai mata bai yi wani tasiri ba
  • Marubuci, Jeremy Bowen
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC international editor

Harin ramuwa da Isra'ila ta kai wa Iran bai kai girman da Shugaban Amurka Joe Biden da sauran ƙawayenta suka yi fargaba ba tun farko.

Sun yi ta bai wa Isra'ilar shawarar ta yi takatsantsan tun bayan harin farko da ta kai wanda ya kashe babban jami'in sojan Iran a birnin Damascus ranar 1 ga watan Afrilu.

Kusan wata shida ke nan tun bayan harin Hamas a Isra'ila, an ci gaba da yaƙi a Gabas ta Tsakiya wanda kuma ya fantsama a gefen iyakar Isra'ila da Lebanon da kuma sauran ƙasashen yankin Larabawa.

Faragabar ita ce cewa yanzu Gabas ta Tsakiya na kan gwiwar faɗawa cikin gagarumin yaƙi, abin da ka iya haddasa bala'i a yankin da kuma duniya baki ɗaya.

Iran ta ce harin bai yi wani tasiri ba a yankin Isfahan.

Rahotonnin farko-farko sun ce ba hari ba ne. Daga baya kuma wani mai sharhi a kafar talabijin ta Iran ya ce makaman kariya na Iran sun kakkaɓe jirage marasa matuƙa da "masu kutse" suka aiko.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar kuma sun wallafa hotunan jiragen da suka kai harin a matsayin abin dariya.

Isra'ila ta kai harin ne a matsayin ramuwa kan wanda Iran ta kai mata ranar Asabar ɗin da ta gabata. Duk da tsawon shekarun da suka shafe suna adawa da juna, wanna ne karon farko da Iran ta kai wa Isra'ila hari daga cikin ƙasarta tun bayan juyin juya-hali a 1979.

Yayin wancan harin, Iran ta harba makamai da jirage marasa matuƙa sama da 300. Garkuwar makamai ta Isra'ila ta lalata kusan dukkansu tare da taimakon Amurka da Birtaniya da Jordan.

Iraniyawan sun bayyana aniyarsu ƙarara, wanda hakan ya sa Isra'ila da ƙawayenta suka shirya wa harin, kuma cikin gaggawa ta bayyana cewa sun kammala ramuwar.

Shugaba Biden ya nemi Isra'ila "ta rungumi nasara" amma ta haƙiƙance cewa sai ta rama.

Tun daga farkon lamarin, hare-haren sun nuna yadda Iran da Isra'ila suka gaza fahimtar juna. Dukkansu ba su yi lissafi da kyau ba, wanda hakan ya ta'azzara lamarin.

Da alama Isra'ila ta zaci Iran ba za ta iya mayar da wani martanin kirki ba ban da kumfar-baki lokacin da ta kashe mata Janar Mohammed Reza Zahedi a birnin Damascus.

Harin da ta kai ta sama ya rusa ginin ofishin jakadancin Iran tare da kashe ƙarin mutum shida.

Iran ta sanar cewa harin tamkar a kan ƙasarta aka kai shi. Isra'ila ta yi iƙirarin cewa ginin ba shi da wata kariya daga dokokin Majalaisar Ɗinkin Duniya saboda dakarun Rundunar Musulunci na taruwa a wurin.

Iran da ƙawayen Isra'ila na ƙasashen Yamma ba su amince da iƙirarin Isra'ilar ba - kuma gwamnatin ta Tehran ta yi fatan Isra'ila za ta haƙura idan ta rama harin.

Shi ma wannan wani rashin lissafin ne.

Idan harin Isfahan bai jawo ƙarin wasu hare-hare ba, to ƙurar da ake ciki yanzu za ta lafa.

Abin da ya faru da tsakar dare zai iya zama yunƙurin Firaministan Isra'ila na ramuwa ba tare da ya sake ɓata alaƙrsa da Shugaba Biden ba.

Idan haka ne kuma, wata tambayar ita ce ko hakan zai sanyaya zuciyar sauran janar-janar na gwamnatin Netanyahu da ke son a kai wa Iran ɗin munanan hare-hare don koya mata hankali.

Ministan Tsaro Itamar Ben Gvir ya ce akwai buƙatar Isra'ila ta nuna "ba sani ba sabo" idan za ta hari Iran. Amma cikin wani saƙo a kafar sada zumunta, ya siffanta harin a matsayin "mitsitsi".

Abin da ya fi dacewa ga yankin, a ra'ayin ƙasashen Yamma, shi ne Iran da Isra'ila su mayar da wuƙaƙensu kube.

Sai dai kuma, ko da a ce ƙarshen wannan rikicin na yanzu kenan, an riga an yi aika-aika.

Iran ta kai wa Isra'ila hari kai-satye, ita ma Isra'ila ta rama kai-tsaye.

Wannan sauyi ne a abin da aka saba kwatantawa da "sharuɗɗan wasan" tsakanin Iran da Isra'ila a rikicin da suka daɗe suna gwabzawa a fakaice.

A ƙarshe dai ta bayyana cewa duk da irin lokacin da suke ɓatawa wajen saka wa juna ido, Iran da Isra'ila ba su da ƙwarewar gane manufar junansu.

A irin wannan duniyar mai sarƙaƙiya, wannan ba abin maraba ba ne.

People are also reading