Home Back

Bamu da wata alaƙa akan dakatar da Ganduje daga jam’iyyar APC – Gwamnatin Kano

dalafmkano.com 2024/5/17

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce basu da wata alaƙa da rikicin cikin gidan da ya kunno kai akan dakatar da Ganduje daga cikin jam’iyyar APC, a Kano.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM a yau Laraba.

Ya ce zargin da jam’iyyar APCn Kano ta yi a kan gwamnatin Kano, kan cewar tana da hannu akan dakatar da shugaban ta na riƙo a matakin ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, zargin bashi da tushe ballantana makama.

A baya-bayan nan ne dai wani sashi na shugabancin jam’iyyar APC, a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, ya bayyana dakatar da Abdullahi Ganduje daga cikin jam’iyyar.

Sai dai daga bisani shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar ya musanta batun dakatarwar inda ya ce ana shirin ɗaukar matakin da ya dace akan wanda ya fitar da sanarwar.

Bature, ya kuma ce lamarin rikici ne na cikin gidan jam’iyyar ta APC, wanda ya kamata su tsaya su gyara, mai-makon mayar da hankali akan gwamnatin Kano, lamarin da ba za suyi nasara ba.

“Tsagin jam’iyyar APCn, Kano suje can kada su ƙara tsomo mu a cikin rikicin su domin bamu da alaƙa da wani rikicin su ko wani abu, “in ji Sunusi”.

Ya kuma ce ko da yaushe jam’iyyar NNPP, mai mulki a jihar Kano burin su shine ci gaba da taimakawa al’ummar jihar ta hanyar damar da ayyukan ci gaban su.

Dawakin Tofa, ya kuma ƙara da cewa Ganduje bashi da tasiri ko da a ƙaramar hukumar sa ballantana kuma azo batun jahar Kano.

People are also reading