Home Back

Rahoto: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Mallakar Lambar Kira A Duniya

leadership.ng 3 days ago
Rahoto: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Mallakar Lambar Kira A Duniya

Kasar Sin ta zama kasa ta farko a duniya mai ikon mallakar lambar kira a duniya, inda ta ba da gudummawar kusan rabin dukkan takardun neman iznin mallakar lambar kira da aka gabatar a shekarar 2022, a cewar wani sabon rahoton kasar Jamus da aka fitar a ranar Juma’a.

An amince da takardun neman iznin mallakar lambar kira miliyan 3.4 a duk duniya a cikin shekarar 2022. Wannan karuwa ce mai ban mamaki daga 635,000 a shekarar 1980, inda daga cikinsu wasu 44 ne kawai aka samu daga kasar Sin, a cewar kungiyar kamfanoni masu binciken magunguna na Jamus (vfa).

An bayyana cewa, kasar Sin ce ke dauke da fiye da karuwar ninki biyar a jimillar takardun neman iznin mallakar lambar kira a cikin shekaru 40 da suka gabata.

Babban masanin tattalin arziki na vfa Claus Michelsen ya ce, ci gaban kasar Sin a matsayin cibiyar kasuwanci da kirkire-kirkire yana da sauri, kana bunkasuwar kimiyyar kasar da ayyuka masu nasaba da lambar kira “ba a taba samun irinsu ba a tarihin tattalin arziki na baya-bayan nan.” (Yahaya)

People are also reading