Home Back

Ana zaben 'yan majalisar dokoki a Faransa

dw.com 6 days ago
Yadda ake zaben kasa a Faransa
Yadda ake zaben kasa a Faransa

Da safiyar wannan Lahadi ne aka bude rumfunan zabe, inda mutum miliyan 49.3 da aka yi wa rajista za su zabi 'yan takara da suke muradi.

Bayanai na cewa kashi 25.9% na mutane sun fito kafin karfe 12 na rana agogon kasar, adadin kuma da ya zarta na zaben da aka yi shekaru biyun da suka gabata a daidai wannan lokacin da kashi 7.5%

Tun a jiya Asabar ne dai 'yan Faransar wadanda ke a kasashen ketare suka kada tasu kuri'ar saboda bambancin lokaci.

Ana kuma sa ran soma samun shigowar bayanan wadanda suka yi nasara jim kadan bayan karfe takwas na yammacin yau Lahadi.

Shugaban Faransar Emmanuel Macron ya kira zaben gaggawa ne dai, bayan gagarumar nasarar da jam'iyyar masu tsaurin ra'ayi ta Marine Le Pen ta samu a lokacin zaben majalisar Turai a farkon wannan wata.

People are also reading