Home Back

Dole Ne Mu Kiyaye Martabar Sarkin Musulmi – Malamai

leadership.ng 2024/8/20
Dole Ne Mu Kiyaye Martabar Sarkin Musulmi – Malamai

Majalisar Matasan Malaman Musulunci ta Arewa ta bukaci ‘yan Nijeriya da su kara himma wajen kiyayewa da mutunta masarautar Sakkwato.

Shugaban Majalisar, Musa Yusuf ne ya bayyana haka a ranar Laraba a Kaduna a wajen wani taron kwana biyu kan matsayar Malaman Arewa na kare martabar Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da kuma alfarmar masarautar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa 19 ne suka halarci taron.

Yusuf ya ce dole ne a mutunta martabar Sarkin Musulmi a matsayin mai kula da halifanci na Musulmai.

Ya ce, Sarkin Musulmin yana wakiltar al’ummar Musulmi a Nijeriya, yana mai gargadin cewa duk wani yunkuri na tozarta mukaminsa za a dauke shi a matsayin wani hari ga Musulmi baki daya.

Shugaban ya bukaci gwamnatin jihar Sokoto da ta mai da hankali kan kalubalen da jihar ke fama da shi, don inganta ilimi, lafiya da tattalin arzikin jihar.

Shi ma da yake nasa jawabin, wani malamin Kano, Abdulmutallib Ahmad, ya shawarci masu rike da sarautun gargajiya da su kauda kai akan siyasa, su baiwa al’ummarsu fifiko.

Ya shawarci shugabannin siyasa da su ji tsoron Allah, su mutunta al’adu da addini.

People are also reading