Home Back

TSADAR RAYUWA: Mazauna Abuja sun jinginar da tukunyar Iskar gas ɗin su sun rungumi gawayi

premiumtimesng.com 2024/4/28
Gwamnatin jihar Nasarawa ta hana siyar da gawayin girki da amfani da shi a faɗin jihar

Wasu mazaunan Babban Birnin Tarayya, Abuja sun bayyana cewa tsananin tsadar rayuwa ya sa sun jinginar da tukwanen iskar gas ɗin su na girki sun rungumi girki da gawayi.

Dalilin yin haka kuwa na da nasaba ne da tsadar iskar gas da ake fama da shi yanzu.

Shi kansa farashin gawayin yayi sama daga naira 3,500 zuwa 4,000 ya koma naira 5,000 zuwa 6,000.

Wata mazauniyar gundumar Gwagwalada Victoria Amosu ta ce tun da gas ya kara kudi ta koma amfani da gawayi da itace.

Victoria ta ce a shekarar 2023 ta siya tukunyar gas mai nauyin 12.5 akan naira 12,000 zuwa 13,000 amma yanzu farashin sa ya kai naira 15,750 zuwa 16,000.

Wani dan kasuwa dake Unguwar Maraba mai suna Dayo Kunle ya ce iyalinsa na amfani da gawayi yanzu saboda yawansu ba zai iya jure siyar Gas ba a wannan lokaci da ake ciki.

“Mukan yi amfani da gas amma sai wajen dumamen abinci kokuma idan ya zama dole.

Gloria Ikenna wace ke sana’ar abinci ta ce itama dole take amfani da gas duk da ko a kullum kaea kuɗi ya ke yi.

“Na bude gidan siyar da abinci a unguwar da aka hana girki da itace ko gawayi. Hakan ya sa dole na ke girki da Gas, kuma ribar da nake samu bai taka kara ya karya ba.

Gloria ta yi kira ga gwamnati da ta rage farashin gas domin tallafawa talakawa da masu sana’a irin nata.

Wata dake bautar kasa NYSC Ogechukwu Ukwuani ta ce tsadar farashin gas ya sa tana amfani da risho da kuma wuta.

“Matsalar ita ce idan aka dauke wuta dole na nemi wani abincin da zan ci domin ba zan iya girki ba.

 
People are also reading