Home Back

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

bbc.com 2024/7/3

Rahoto kai-tsaye

MDD ta yi kakkausar suka kan kisan Falasɗinawa

Gaza

Asalin hoton, Reuters

Babban jami'in diflomasiyyar Tarayyar Turai, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan Falasɗinawa da sojin Isra'ila suka yi lokacin da suka kai samamen kuɓutar da waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su a a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat.

Josep Borrell ya yi maraba da samun ƴancin Isra'ilawan, amma ya ce bai kamata a kawar da kai ba ga adadin waɗanda suka mutu wajen ceto Isra’ilawan.

Rahotanni sun ce a karon farko an samu mutane da suka fusata da Hamas, domin kuwa akwai wanda a cikin wata biyu da suka wuce ya rasa iyayensa, yanzu ma ɗan uwansa ya rasu, kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ‘’me ya sa za ku ajiye waɗanda ku ka yi garkuwa da su a sansanin ƴan gudun hijira?’’

People are also reading