Home Back

Fargaba da addu'o'i a birnin Sudan da ke cikin mamaya

bbc.com 2024/5/19
..

Sa'o'i 7 da suka wuce

Barazanar farmaki ta haifar da matsanancin fargaba a El Fasher, babban birni a Yammacin Darfur da ke Sudan, kuma na ƙarshe cikin manyan biranen da har yanzu suke ƙarƙashin ikon sojoji.

“Gabadaya muna rayuwa cikin tsoro da damuwa game da abin da zai faru nan ba da jimawa ba,” in ji Osman Mohammed mai shekara 31, wanda kuma malamin makaranta ne da ke koyar da Turancin Ingilishi.

Shi ma Mohammed Ali Adam Mohamed mai shekara 36, wanda ɗan kasuwa ne, mai ƴa ƴa biyar ya bayyana abinda yaƙi ke nufi.

“Idan aka yi arangama tsakanin dakarun RSF da Sojoji a cikin gari, mu fararen hula ne muke ji a jikinmu” kamar yadda ya shaidawa BBC.

Mummunan yaƙin basasar Sudan ya samo asali ne kusan shekara guda da ta gabata, bayan da wasu manyan sojojin ƙasar biyu da suka yi juyin mulki suka raba gari.

Kafin yanzu El Fasher ya tsira daga mummunan hari da kashe-kashen ƙabilanci da suka yawaita a Dafur yankin da ya kasance cibiyar dakarun RSF.

Sai dai tun a tsakiyar watan da ya gabata, dakarun RSF suka yi wa birnin ƙawanya, bayan ya kasance mafakar dubban mutanen da suka rasa matsugunansu, ciki har da waɗanda suka tsere daga wasu yankunan da dakarun suka ƙwace.

A halin yanzu luguden wuta da arangama a birnin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 43, cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Yayin da jama'a suke jiran ganin yadda rundunar RSF za ta ƙaddamar da cikakken hari a birnin, sun fi mayar da hankali kan yadda za su tseratar da rayuwarsu.

Osman na shirin yin aure don fara sabuwar rayuwa da masoyiyarsa, to amma yanzu hankalinsa ya karkata wajen neman abubuwan more rayuwa na yau da kullum, kamar yadda ya shaida wa BBC

“Rayuwa ta yi tsananin wahala saboda rashin tsaro da rashin hada-hadar kuɗaɗe da ma rashin kuɗin gabaɗaya,” abinci da ruwa da zirga-zirga da ilimi komai ya yi tsada.

“Masu hannu da shuni sun ɓace, “kashi 80 na ƴan ƙasar a yanzu duk talakawa ne,” in ji Mohammed

Dole ya rufe shagonsa na sayar da kayan masarufi ya buɗe wani ƙarami, tun farkon fara rikicin bayan ankai wa shagon hari. Kasuwanci ya durƙushe sakamaon hauhawar farashi.

“Ana samun hauhawar farashi da zarar an garƙame hanyoyi,”

Babu hasken lantarki ga kuma tsananin rashin ruwa, saboda rashin mai da kuma ƙaruwar mabuƙatasaboda kwararar waɗanda yaƙin ya ɗaiɗaita.

“Farashin ruwa ya ƙaru,” cewar Hussein Osman Adam, wanda ke tuƙa motar jigilar fasinjoji da kayan abinci a wasu lokuta.

Hussein na fama da lalurar ciwon siga, ga shi kuma kayan gwajin jini sun ƙare.

“A yanzu dai muna jiran tsammani” in ji shi.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka na hasashen yanayin zai tsananta.

Sun fitar da gargaɗin abin da cikakken hari zai haifar a yankin da ke dab da faɗawa yunwa.

A farkon wannan wata ne wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta bayyana cewa harin zai kasance tamkar kisan kare dangi, masifa kan masifa.

Wannan hasashen ya ginu ne a kan rahotanni daga wasu garuruwan da dakarun RSF da kawancen mayaƙan sa kai na Larabawa suka kai wa farmaki inda suka sace kaya da ƙaddamar da harin ƙabilanci da kuma cin zarafin mata.

Kwamandojin RSF sun ƙaryata waɗannan zarge-zarge. Sun kuma ce suna da damar kare kansu daga harin sojoji bayan sun zargi sojojin da kashe fararen hula da bama-bamai da gangan.

Ɗaya daga cikin dalilan da suka hana su karɓe ikon El Fasher har yanzu su ne, saboda ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a can sun haɗa kai da sojojin ƙasar Sudan da kuma manyan ‘yan tawaye daga ƙabilar Zaghawa waɗanda suka sha alwashin yin nasara a kan dakarun RSF.

Ƙungiyar Likitoci ta Duniya (MSF), ta shaida wa BBC cewar ta yi wa majinyata 125 da suka samu raunuka daga harin sojoji ta sama magani.

To amma ta ɗauki watanni tana gargaɗin rashin abinci mai gina jiki a sansanin yan gudun hijira na Zamzam da ke Kudancin El Fasher, inda ya zama matsugunin wadanda yakin ya raba da muhallansu.

Claire Nicolet shugabar sashen agajin gaggawa a kungiyar likitoci ta duniya MSF a Sudan ta ce karuwar tashin hankali ta sanya komai ya yi wahala.

Musamman yadda a 'yan watannin nan aka tilastawa mutanen da suka tsere daga yankunan shiga cikin birnin El Fasher, inda aka basu matsugunai a makarantu da wuraren da ake gudanar da taruka.

Fayza Ibrahim Osman mai kula da sansanin yan gudun hijira ta Tambasi ce.

Ta bayar da labarin yadda ta tsere daga gida a Arewacin garin.

Cibiyar na 'dauke da mutanen da suke fama da lalurar da suke neman magani. To amma rashin abinci ne babbar matsalar da ta fi damun mutane, Kungiyar Agaji ta Red Cross ta dakatar da kai abinci sau biyu da ta ke yi.

A ranar Alhamis ana gudanar da Karatun Alkur'ani don rokon Allah ya tsayar da yakin.

“Abun tashin hankali shi ne yadda mutane suke fama da damuwa saboda yawaiatr tashe-tashen hankula,” kamar yadda Mohammed mai sayar da kayan masarufi ya bayyana.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane na fargabar a kashe su idan suka yi yunkurin guduwa, amma Kungiyar Likitoci ta Duniya MSF ta ce akwai wasu tsirarun wurare da za su iya zuwa.

People are also reading