Home Back

Ba Wanda Zai Iya Keta Ka’Idar “Kasar Sin Daya Tak a Duniya”

leadership.ng 2024/6/26
Ba Wanda Zai Iya Keta Ka’Idar “Kasar Sin Daya Tak a Duniya” 

A ‘yan kwanakin baya, Lai Ching-te, mutumin da ya yiwa kansa lakabi da wai “Mai aikin ‘yantar da Taiwan”, ya zama jagoran yankin Taiwan. Kuma a jawabinsa na kama aiki, ya yi shelar cewa, wai yankin Taiwan na samun ‘yancin kai, inda ya yada jita-jitar cewa, babban yankin Sin ya yi barazanar soja, biyowa bayan yunkurin ware yankin Taiwan daga kasar Sin, ta hanyar amfani da karfin wasu sassan ketare, da kuma karfin soja. 

A sa’i daya kuma, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, ya taya Lai Ching-te murnar kama aiki, inda Amurka ta tura wakilinta don halartar bikin rantsuwarsa. Matakin dai ya kasance wani sabon wasan kwaikwayo ne da wasu ‘yan siyasar Amurka, da na yankin Taiwan suka gudanar, inda suka zauna a inuwa guda. Sai dai duk da haka, ba za a iya keta ka’idar “Kasar Sin daya tak a duniya” ba, wadda kasashen duniya ke bi.

Manazarta sun nuna cewa, Lai Ching-te, ya fadi duk abin da yake so a cikin jawabinsa ne, sakamakon samun amincewar Amurka, duk da cewa Amurka ba ta da karfin gwiwa kansa a tsawon lokaci, amma tana son gabatar da ra’ayin samun ‘yancin kan Taiwan daga bakinsa, don jiran martanin da kasar Sin za ta mayar.

Baya ga hakan, ‘yan siyasar Amurka suna yunkurin neman amincewa daga masu kada kuri’u bisa batun Taiwan, duba da cewa, bana za a yi babban zabe a Amurka.

Batun Taiwan, harkokin cikin gidan kasar Sin ne, wanda ya kasance muradi mai tushe na kasar, kuma tushen siyasa na huldar kasashen Sin da Amurka, kana jan-layi ne na farko da ba zai yiwu a tsallaka shi ba, a dangantakar Sin da Amurka.

A watan Nuwamban bara, yayin ganawar shugabannin kasashen biyu a San Francisco, shugaban Amurka ya yi alkawarin kin amincewa da goyon bayan ware Taiwan daga kasar Sin, kuma a watan Afrilu na bana, yayin tattaunawar shugabannin biyu ta wayar tarho, bangaren Amurka ya nanata manufar “kasar Sin daya tak a duniya”. Amma daga bisani Amurka na yin fuska biyu, kuma ta yi amai ta lashe.

Yanzu haka, babban yankin kasar Sin na jan ragamar bunkasuwar huldar babban yankin da yankin Taiwan, yana kuma da aniyya, da karfin kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, da ma kiyaye ikon mulkin kasar da cikakkun yankunan ta. Ba shakka, kasar Sin za ta samu dunkulewa, kuma ba wanda zai hana ta cimma wannan baru. (Amina Xu)

People are also reading