Home Back

‘Hassan da Husaini ne?’ Gaskiyar Abin da Abba Ya Fada da Ya Hadu da Sarkin Kano

legit.ng 2024/5/17
  • Abba Kabir Yusuf ya zauna da Sarkin Kano a ranar hawan Nasarawa da ya gudana ranar Juma’a a sallar nan
  • Mun yi bincike ganin ana yada cewa Mai girma Gwamnan jihar Kano ya kira Sarki Aminu Ado Bayero da Husaininsa
  • Zancen ya jawo surutu ne ganin wasu suna ganin za a bibiyi dokar da ta kawo Mai martaba Aminu Ado Bayero a 2019

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A ranar Juma’a aka fara yawo da jita-jita cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna tagwaye suke da Sarkin Kano.

An kirkiro labarin ne bayan Mai girma Abba Kabir Yusuf da Mai martaba Aminu Ado Bayero sun hada a ranar hawan Nasarawa.

Sarkin Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarki Aminu Ado Bayero a Kano Hoto: Salisu Yahaya Hotoro Asali: Facebook

Ana hawan karamar sallah a Kano

A halin yanzu ana bukukuwan sallah, a Kano abin ya fi armashi saboda kwanakin da ake shafewa ana hawa domin wannan biki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa al’ada, Sarkin Kano ya kan ziyarci fadar gwamnatin Kano a ranar hawan Nasarawa da ake yi kwanaki biyu bayan idi.

Wannan karo abin bai canza ba, Sarki Aminu Bayero da mutanensa sun je fadar gwamnati, an yi zama a dakin taron Africa House.

Jim kadan bayan nan sai wata gidan rediyo da ke Kano ta rahoto gwamna Abba ya ce shi da Sarki tamkar Hasan da Husaini ne.

Legit Hausa ta bibiyi gaskiyar abin da ya faru, ta fahimci an juya kalaman gwamnan a lokacin da wasu ke kiran a sauke Mai martaba.

Abba Yusuf yana cikin jikokin Ibrahim Dabo da ke sarautar Kano, jika ne ga ‘Dan makwayon Kano, amma bai yi wannan magana ba.

Kakan Abba ya rike Hakimi a Gaya a lokacin da Abdullahi Bayero yake sarki a Kano.

Fai-fan da Salisu Hotoro ya wallafa a Facebook ya nuna gwamnan ya ce gwamnati da masarauta tagwaye ne wajen mulki a Kano.

"Masarauta da gwamnati Hasan da Husaini ne wajen gudanar da aikin gwamnati."

- Abba Kabir Yusuf

Mai taimakawa gwamnan a kafofin sadarwa na zamani ya karyata wannan jita-jita, ya ce babu inda gwamna ya fadi haka a jiya.

Hotoro ya ce Malam Usamatu Salga, Alhaji Shehu Sagagi da kwamishinan addinai ne suka yi magana bayan gwamna da Sarkin Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading