Home Back

ƘAƘUDUBAR ƘARIN ALBASHI: ‘A daina yaudarar jama’a, ba wanda ke iya dogara da albashin sa a Najeriya’ – Majalisar Tarayya

premiumtimesng.com 2024/6/26
DAGA WAKILAN JAMA’A:  ‘Yan Majalisa sun manta da matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa, sun haƙiƙice kan yi wa ƙungiyoyin kishin jama’a takunkumi

A zaman Majalisar Tarayya na ranar Laraba, ta koka kan yadda dambarwar ƙarin albashi ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa tsawon shekaru da dama.

Mambobin majalisa da yawa ɗaya bayan ɗaya sun yi kira da a daina maganar ƙarin mafi ƙanƙantar albashi, maimakon haka, a yi maganar ƙarin wadataccen albashin da zai ishi ma’aikata.

Ɗan Majalisar Tarayya Ali Madaki, ɗan NNPP daga Kano, ya jawo ayoyi a cikin Kundin Dokokin Najeriya, inda ya nuna wajibcin yi wa ma’aikata ƙarin albashi wadatacce.

Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda, ɗan PDP daga Jihar Ribas, ya ragargaji gwamnatin tarayya dangane da rashin ɗaukar albashin ma’aikata da muhimmanci.

“Shin Gwamnatin Tarayya ta na cika aikin da ya wajaba a kan ta. Shin muna samar da tsaro? Shin muna samar da kayan rayuwar jin daɗi ga al’umma? Amsa ita ce ‘a’a’.

“Tsawon shekaru da dama kenan, ana ta magana kan mafi ƙanƙantar albashi, maimakon a yi batun ƙarin wadataccen albashi. Gaskiyar magana babu ma’aikatacin da ke iya dogara da albashin sa kaɗai don ya rayu.

“Ta yaya ma’aikaci zai iya yin aiki ana biyan sa Naira 50,000.00 a wata? Nawa zai biya kuɗin mota zuwa wurin aiki?”

Bayan janye yajin aiki dai Ƙungiyar Ƙwadago ta ce ba za ta amince Gwamnati ta ƙara ‘yan dubunnai kan Naira 60,000 da ta yi ba.

Yayin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bai wa Ministan Harkokin Kuɗaɗe umarnin sa’o’i 48 ya kai masa ƙarin kuɗin mafi ƙanƙantar albashi domin ya sa hannu, Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC ta bayyana cewa ba fa za ta amince a yi ƙarin wasu ‘yan dubunnai a kan Naira 60,000 ɗin da Gwamnatin Tarayya ta ƙara ba, kafin tafiya yajin aiki.

Shugaban Ƙungiyar TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka, ranar Litinin cikin wata tattaunawar da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Ya ce su ba wai sun tsaya lallai sai Naira 494,000 za a biya a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba. “To amma dai gwamnati ta yi wani abin a zo a gani, wanda kowa zai iya cewa ta yi nata ƙoƙarin.” Inji shi.

Da aka tambaye shi adadin da ya kamata gwamnati ta biya matsayin mafi ƙanƙantar albashi sai ya ce, “ya kamata dai kwamitin gwamnatin tarayya ya fito da wani adadi wanda zai tafi kafaɗa da kafaɗa da halin da tattalin arzikin ƙasa da masifar tsadar kayan abincin da ake fuskanta.

“Saboda mun shaida masu ba za mu amince da irin ƙarin Naira 1, Naira 2 ko Naira 3,000 uku kamar yadda ta riƙa yi a baya ba. Sannan daga nan sai ta riƙa alƙawarin da ta san ba iya cikawa za ta yi ba.”

Ya ce ƙarin albashin da za a yi tilas sai ya yi daidai da abin da Naira 30,000 za ta iya saye a 2019 da kuma abin da Naira 18,000 za ta iya saye 2014.

NLC da TUC dai sun bai wa gwamnatin tarayya kwanaki biyar domin a sami tsayayyen farashi, ko kuma su ci gaba da yajin aiki.

People are also reading