Home Back

Sabon Tsari: Alhazan Nijeriya Zasu Daina Daɗewa A Saudiyya

leadership.ng 2024/7/1
Sabon Tsari: Alhazan Nijeriya Zasu Daina Daɗewa A Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON, ta aiwatar da wani sabon tsari da nufin rage yawan lokutan da alhazan Nijeriya ke yi a ƙasar Saudiyya a lokacin aikin Hajji. Shugaban hukumar Malam Jalal Arabi ne ya bayyana hakan, da yake jawabi jim kaɗan bayan isar sa filin jirgin saman Yarima Mohammed Bin Abdulaziz da ke birnin Madina, ya ce hukumar ta samu nasarar kammala jigilar alhazan Najeriya ɗari bisa ɗari zuwa Madina.

Arabi ya kara da cewa, cimma wannan buri na iya taimakawa wajen takaita zaman alhazan Najeriya baki daya, waɗanda a tarihi suke shafe tsawon lokaci a ƙasar Saudiyya, inda suke yi ta kai-kawo, yayin da aka kwashe alhazan wasu ƙasashe cikin gaggawa.

Arabi ya yabawa fadar shugaban ƙasa, da majalisar dokokin ƙasar, da kuma jiragen dakon fasinja bisa goyon baya da haɗin kai, wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen samun nasarar aikin hajjin.

NAHCON ta tabbatar da cewa dukkan maniyyatan Najeriya sun kasance a ƙasar Saudiyya sa’o’i 72 kafin rufe sararin samaniyar Saudiyyar, lamarin da ya tabbata ta hanyar haɗin gwuiwar masu ruwa da tsaki na gwamnati da masu zaman kansu.

Hukumar ta NAHCON ta kuma tanadi cikakken tsarin ciyar da alhazai da kula da lafiyar alhazai a lokacin aikin hajji daga ranar 13 ga watan Yuni.

Arabi ya bayyana cewa hukumar ta isa Makkah domin tantancewa tare da magance duk wata matsala da aka samu dangane da masu ba da hidima, yana mai jaddada cewa ba za su yi sakaci da Alhazan Najeriya ba balle su wulakanta ba.

People are also reading