Home Back

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 5 a Taraba

premiumtimesng.com 2024/5/15
MATSALAR TSARO A KATSINA: ‘Yan bindiga sanye da hijabi sun sake afka wa jami’an tsaro a yankin Batsari

Rundunar sojin Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘6 Brigade’ sun kashe ‘yan bindiga 5 sannan sun kwato makamai daga hannun maharan a jihar Taraba.

Rundunar ta sanar da haka ne a shafinta na sada zumunta na yanar gizo ranar Talata.

Bisa ga sanarwar da rundunar ta fitar dakarun sun kashe maharan yayin da suke kokarin yin garkuwa da mutane a Wukari dake hanyar Tor – Tse da Takum a safiyar Talata.

Dakarun sun yi nasarar kashe maharan tare da kwato makamai da dama daga hannun su ne bayan samun bayanan sirri da suka yi.

“jami’an tsaron sun kashe mutum biyar daga cikin maharan sannan sun kwato makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47, Pump action 1 da harsasan AK-47 guda biyu.

People are also reading