Home Back

IPMAN: Farashin Litar Man Fetur Ya Tashi Zuwa N2,000 a Jihar Arewa, An Gano Dalili

legit.ng 6 days ago
  • Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas sakamakon yajin aikin ƙungiyar dillalan mai IPMAN
  • Shugaban IPMAN reshen Adamawa/Taraba, Alhaji Dahiru Buba, ya ce ba gudu ba ja da baya a yajin aikin da suka fara har sai kwastan ta daina muzguna masu
  • Wasu mazauna Yola sun bayyana halin wahalar da suka wayi gari a ciki na rashin ababen hawa da tsadar kuɗin sufuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) reshen Adamawa/Taraba ta bayyana kudurinta na ci gaba da yajin aikin da take yi.

IPMAN ta bayyana cewa za ta ci gaban da yakin aikin da take yi a Adamawa ba gudu ba ja da baya duk kuwa da cewa litar fetur ta kai N2,000.

Gidan mai.
Yajin aikin IPMAN ya jawo tashin farashin litar man fetur a jihar Adamawa Hoto: NNPC Asali: Facebook

Shugaban kungiyar IPMAN na jihar, Alhaji Dahiru Buba, ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Yola ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yajin aikin ya biyo bayan muzgunawa mambobin IPMAN da kuma kwace musu motocin mai da jami’an kwastam ke yi ba bisa ka’ida ba, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, hakan ya jawo masu asara, ƙarancin mai da hauhawar farashin fetur, don haka yajin aiki zai ci gaba har sai kwastam sun daina muzgunawa dillalan mai.

Rahotanni sun bayyana cewa yajin aikin IPMAN ya haifar da tsadar man fetur da kuma taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a jihar Adamawa.

Wani ɗan Yola, Abubakar Muhammed ya shaidawa NAN cewa ma'aikata da sauran jama'a sun wayi gari cikin wahalar samun ababen hawa.

Muhammad ya ce kuɗin sufuru ya yi tashin gwauron zabi domin a yanzu mutane na biyan N700 zuwa wurin da aka saba biyan N300,000 a baya.

NAN ta gano cewa mafi akasarin gidajen mai a rufe suke a birnin Yola yayin da masu motoci da babura suka rasa wani zaɓi face sayen mai a wurin ƴan bunburutu.

NLC ta aika saƙo ga Tinubu

A wani rahoton kuma ƴan kwadago sun roki Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da soyayyar da yake masu yayin yanke sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.

Mamban kwamitin mafi karancin albashi kuma wakilin NLC ya buƙaci shugaban ƙasa ya amince da buƙatar ƴan kwadago ta N250,000.

Asali: Legit.ng

People are also reading