Home Back

Binciken CGTN: Kusan Kashi 90 Cikin Dari Sun Goyi Bayan Habaka Hadin Gwiwar Inganta Aikin AI

leadership.ng 3 days ago
Binciken CGTN: Kusan Kashi 90 Cikin Dari Sun Goyi Bayan Habaka Hadin Gwiwar Inganta Aikin AI

A ranar Litinin ne babban taron MDD karo na 78, ya amince da kudurin da kasar Sin ta gabatar tare da daukar nauyin sama da kasashe 140, a kan karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen inganta aikin fasahar kwaikoyon tunanin dan Adam ko AI a takaice. Bisa wani binciken da kafar CGTN ta gudanar ta yanar gizo, akasarin masu bayyana ra’ayinsu sun yi tsokaci kan kokarin da Sin ke yi wajen inganta hadin gwiwar AI a duniya. Kashi 89.72 cikin 100 na wadannan mutane sun yaba da matsayin kasar Sin na cewa, ya kamata ci gaban AI ya kiyaye “bin tsarin ka’idojin dan Adam,” da sa kaimi ga samar da basira mai fa’ida, da kuma amfanar bil Adama.

Kafar CGTN ta fitar da sakamakon kuri’un na jin ra’ayin jama’a cikin harsunan Turanci, Spanish, Faransanci, Larabci da Rashanci, tare da samun kuri’un da mutane 9481suka kada cikin sa’o’i 24. (Yahaya)

People are also reading