Home Back

Tattaunawa Da Mika’il Isah (Gidigo) Da Ya Kwashe Shekara 25 A Fagen Fina-finan Hausa

leadership.ng 2024/5/14

Abin Da Ya Sa Ya Fi Son Fim Dinsa Na ‘Furuci’

Tattaunawa Da Mika’il Isah (Gidigo) Da Ya Kwashe Shekara 25 A Fagen Fina-finan Hausa

Shahararrem jarumin daya ga jiya ya ga yau a fannin fina-finan Hausa, wanda ya shafe tsahon shekaru ashirin da biyar 25 cikin masana’antar shirya fina-finai ta kannywood wato MIKA’IL ISAH BIN HASSAN wanda aka fi sani da GIDIGO.

Ya bayyana wa masu karatu irin fadi-tashin da suka yi tun kafin fitowar kungiyoyi da kuma kamfanonin shirya fina-finan Hausa wadanda ke tafiya a yanzu, ya kuma bayyana ra’ayinsa game da yadda tsarin siyasar yanzu ke tafiya, har ma da sauran wasu batutuwan da suka shafi rayuwarsa da kuma sana’arsa ta fim. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi?
Sunana Mikail Isah Bin Hassan, sannan kuma ana kira na da Gidigo a cikin wasan kwaikwayo na dabe.

Ko za ka iya fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
To ni dai an haife ni 16 ga watan December a shekarar 1975 a garin Kano, amma asalina ni mutumin Maigatari ne ta Jihar Jigawa, na dan yi karatun zamani dana addini, haka kuma na dan yi kwasakwasai a nan gida Nijeriya da kuma wasu kasashen waje.

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood?
‘Well’, muna yara muna kallon shirin su Danmagori wannan ne abin da ya fara ba ni sha’awa har na tsinci kaina a harkar wasan dabe, mun kafa kungiya lokacin muna jami’a wacce muke gabatar da wasan dabe, wata rana an gayyaci Danmagori a ranar makon Hausa, sai muka gabatar da wasan dabe, da ya gani sai ya yi mani magana ya ce zai yi kyau a ce na shiga harkar fina-finai, to daga nan na fara.

Idan na fahimce ka daidai kana so ka ce ba ka sha wahala ba wajen gwagwarmayar shiga harkar, ko ya abun yake?
‘Well’, a lokacin ai babu kamfanonin fina-finai kamar yanzu, a da can kungiyoyi ne, saboda haka ko da na shigo ta kungiya na fara, sunan kungiyar ‘Jigon Hausa’, kungiyoyi ne suke yin fina-finai, amma daga bisani kuma sai kamfanonin fina-finai suka bulla, babu wata harkar da mutum zai yi ta face ya samu wani kalubale ko yaya yake.

Wanne irin kalubale ka fuskanta a wancen lokacin?
A wannan lokacin mafiya yawan kalubalen da na samu daga gida ne, domin suna ganin kamar muna bata wa kanmu lokaci ne kawai.

Idan na fahimce ka, kana so ka ce lokacin da ka fara sanar wa iyayenka kana sha’awar shiga harkar, ka fuskanci kalubale daga gare su kenan, ko ya abun ya kasance?
Kusan haka ne, domin suna ganin ta yaya mutum zai dauki Dirama a matsayin sana’a, zuwa wani lokaci kuma suka fahimci yadda abin yake.

Tsawon shekara nawa ka yi a wancen lokacin kana dirama, kafin a fito da sabon tsarin bude kamfanoni da kuma kungiya?
Na kai kusan shekara biyu ina yi.

Daga wancen lokacin kawo i-yanzu za ka yi shekara nawa da fara fim gaba daya?
Na kai shekara ashirin da biyar 25.

Ka yi fim sun kai kamar guda nawa?
A gaskiya ba zan iya kirga su ba.

Da wanne fim ka fara?
Na fara da fim din ‘Idan Kunne Ya ji’.

Wanne sako fim din ke isarwa, kuma wanne rawa ka taka cikin fim din?
Sakon yadda samari ke yaudarar ‘yan mata musamman ‘ya’yan talakawa wadanda suke mabukata, na taka rawar daya daga cikin jaruman da suka ja labarin.

Ko za ka iya fado wa masu karatu kadan daga cikin fina-finan da ka fito?
Eh! akwai; Furuci, Mashi, Sunduki, Sauna, Kalas, da dai sauransu, dan ba zan iya tuna su ba.

Idan aka ce ka zabi guda cikin fina-finan da ka fito wanne za ka dauka, kuma me ya sa?
‘Well’, Furuci domin da shi na yi suna.

Kamar wanne bangare ka fi maida hankali akai wajen yin fina-finai?
Bangaren Daraktin duk da yake ni dan koyo ne.

A fina-finai akwai bangarori daban-daban kamar; bangaren barkwanci, da kuma siyasa, da soyayya da dai sauransu, kai wanne ka fi maida hankali a kai?
Ni dan kasuwa ne, saboda haka fim ‘business’ ne, kamar yadda dan kasuwa zai saka kudinsa ya yi kasuwanci haka ma fim yake, a bangaren siyasa kuma ni ban yarda da irin tsarin siyasar da ake yi a Afrika ba, tsarin ne kawai na danniya ba wai dan talaka ake yin ta ba sai don biyan bukatar wasu tsiraru.

Misali; za ka ga wasu sun fi karkata da yin fim iya fina-finan barkwanci kawai, wasu kuma sun fi son su fito a fina-finan da aka gina shi a kan siyasa, wasu kuma fannin soyayya, da dai sauransu, kai kamar wanne bangare kafi maida hankali akai wajen fitowa?
Kowacce rawa aka ba ni zan taka, ai shi mai sana’a baya zabi sai abin da kasuwa ta ba shi.

Ya za ka bambanta wa masu karatu fina-finan baya dana yanzu, tare da bayanin yadda wasan dabe yake a wancen lokacin?
Fim sana’a ce da ake ba da labari a cikin hoto, shi kuma wasan dabe labarin ake bayarwa a gaban masu kallon. Banbancin fina-finan baya ko kuma na ce dirama shi ne kayan aiki da kuma kasuwa.

Wadanne irin nasarori ka samu game da fim?
An samu nasorori da dama.

Kamar wadanne irin nasarori kenan?
Wannan kuma ai sirri ne.

Ko kana da ubangida a cikin masana’antar Kannywood?
Eh Marigayi Director Tijjani Ibraheem Allah ya gafarta masa.

Da wa ka fi so a hada ka a fim?
Da Kowa.

Wanne fim ne ya fi ba ka wahala a cikin fina-finan da ka fito, kuma me ya sa?
Fim din Sauna, saboda yanayin labarin.

Wadanne jarumai ne suke burge ka kafin shigarka masana’antar da kuma bayan shigarka?
Danmagori da Barmo sai kuma Kasimu Yaro.

Misali ka zama shugaban ‘yan Kannywood, shin wanne irin gyara za ka kawo tare da ci gaba cikin masana’antar?
AI ni ba dan Kannywood bane, ni ‘filmmaker’ ne.

Mene ne burinka a nan gaba?
Ya zama ya bunkasa fiye da yadda yake a yanzu.

Me za ka ce da masu karanta wannan hirar taka?
Ni dan Adam ne zan iya yin kuskure, saboda haka idan suka ga na yi kuskure to su yi min uzuri.

Muna godiya
Ni ma na gode

People are also reading