Home Back

Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Shiga Ganawar Sirri Kan Matakin Da FEC Ta Ɗauka

leadership.ng 2024/7/5
Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Shiga Ganawar Sirri Kan Matakin Da FEC Ta Ɗauka

Mambobin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC da TUC sun kira wani taron gaggawa domin tattaunawa kan matakin da majalisar zartarwa (FEC) ta ɗauka na jinkirta sabon mafi ƙarancin albashi. An shirya taron ne da karfe 10:00 na safiyar yau Laraba a gidan ma’aikata.

Taron gaggawar ya biyo bayan sanarwar da FEC ta fitar, wanda ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya bayar na cewa an magance duk wasu batutuwan da suka shafi maƙasudin abinda ke cikin takardar biyan mafi karancin albashi.

Idris ya bayyana cewa an ɗage matakin ne domin ba wa shugaba Bola Tinubu damar tuntubar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da ƙananan hukumomi, daga Jihohi, da ƙungiyoyi masu zaman kansu, da kuma ƙungiyoyin kwadago, kafin ya miƙa wa majalisar dokokin mataki ya karshe a hukumance.

Wani babban jami’in ƙungiyar ta NLC, wanda ya buƙaci sakaye sunan sa, ya bayyana cewa shugabannin cibiyoyin ƙwadagon biyu za su yi taro domin daidaita matsayarsu kan batun mafi ƙarancin albashi kafin tuntuɓar shugaban ƙasar.

Ana ganin wannan taro yana da matuƙar muhimmanci, musamman ganin cewa a kwanakin baya ƙungiyoyin ƙwadagon sun gudanar da yajin aiki na kwanaki biyu domin matsawa gwamnati biyan bukatunsu dangane da mafi ƙarancin albashi.

People are also reading