Home Back

Alamomin Kansar Mama Ta Maza

leadership.ng 2024/5/10
Alamomin Kansar Mama Ta Maza

Galibi mata aka fi sani da ciwon kansar mama, amma kuma likitoci sun bayyana cewa maza ma na iya kamuwa da cutar.

Akalla alamomin kansar mama ta maza (Breast Cancer), sun kai guda bakwai ko ma fiye da haka; kamar yadda binciken masana lafiyar ya tabbatar, wadanda suka hada da:

– Fitowar kaluluwa a kan mama: Guda daga cikin wadannan alamomi na kansar mama shi ne, fitowar kaluluwa daga jikin maman da namiji tare da yi masa matukar zafi.

– Haka nan, wata alama ta kamuwa da wannan cuta ita ce, ganin maman wanda ke dauke da wannan cuta ya rika yin ja.

– Sa’annan, mutum zai rika yawan jin zafi a maman nasa da radadi da zugi tare da ganin canji na kamannin maman nasa, wato kalar maman za ta canza kacokan.

– Har ila yau, ana samun fitar ruwa daga maman wanda yake dauke da wannan cuta. Za a rika ganin ruwa yana fita kai tsaye ta kan maman.

– Bugu da kari, duk dai a cikin wadannan alamomi na kamuwa da wannan cuta, a kwai batun saba; mai dauke da wannan cuta, zai ga maman nasa yana yin saba fatar tana fita.

– Kazalika, wadannan alamomi sun hada da shigewar kan maman ciki. A nan, kan maman ne yake shigewa ciki tare da yin ciwo kwarai da gaske.

– Sai kuma kumburin shi kansa maman, wato maman ne ke kumbura yana yi wa mutum ciwo tare da yi ma zugi, ta hanyar da zai hana shi barci da sukuni baki-daya.

Saboda haka, duk wanda ya ci karo da wadannan alamomi guda bakwai, wadanda sankarar mama ke zuwa da su; sai ya yi maza ya garzaya zuwa asibiti; domin a auna shi.

Haka zalika, ba lallai ne don ka ga guda daga cikin wadannan alamomi ya kasance ka na dauke da wannan cuta ta sankarar mama ba, akwai wadansu cututtukan da suke zuwa da ire-iren wadannan alamomi.

People are also reading