Home Back

ƘANƘANTAR ALBASHI, ƘUDIN WUTA: Kungiyar Kwadago za ta fara yajin aikin gama gari ranar Litinin

premiumtimesng.com 2024/7/3
Yajin Aikin NLC: Cin zalin Talaka ko amfani da Talaka don biya wa kai buƙata

Kungiyar Kwadago ta bayyana cewa za ta tsunduma yajin aikin gama gari ranar Litinin 3 ga Yuni.

Kungiyar ƙarkashin shugabanta Ajaero ta bayyana cewa ba ta cimma matsaya ba game da yarjejeniyar ƙarancin albashi da kuma rage tsadar wutar lantarki da ake fama da shi a ƙasar.

” A zaman taron da muka yi, babu gwamna ko ɗaya da ya halarci taron, haka kuma babu wani minista in banda ƙaramar ministar Kwadago Nkiruka Onyejiocha.

” Haka nuni cewa maganar ƙarin albashin ba ta ɗaɗa su da ƙasa ba ko kaɗan, ba ita ce a gaban su ba.

Kungiyar ta ce tunda gwamnati ba ta ga amfanin zaman ba, suma za su nuna wa gwamnati cewa lallai sai sun tilasta ta ta yi abinda ya dace, wato ta ƙara albashi da rage wutar lantarki.

Kungiyar kwadago ta ce lallai a dawo da kuɗin wutar lantarki baya, wato kamar yadda yake a da can.

Ta gudanar da zanga-zanga amma gwamnati ta yi biris da ita.

” Mu fa talakawa ne a gaban mu, ba zamu yi ƙasa a guiwa ba har sai mun tilasta gwamnati ta yi wannan ƙari sannan kuma wutar lantarki ya koma yadda yake a baya.

” Wannan shine matsayar mu muma babu gudu ba ja da baya, yajin aiki za a fara shi. Saboda haka gwamnati ta kwan da shiri. Kuma ba za a janye ba sai an biya mana buƙatun mu duka.

People are also reading