Gwamnatin Abba Ta Bayyana Matsayarta Kan Tarar N10m da Aka Sanya Mata Kan Aminu Ado
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ƙi amincewa da cin tarar Naira miliyan 10 da kotu ta umarci ta biya saboda take haƙƙin ɗan Adam na Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
A ranar Juma’a ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta sanya tarar a kan gwamnatin Kano.
Sai dai a yayin wata ganawa da manema labarai a gidan gwamnati inda gwamnan ya samu wakilcin Antoni Janar na jihar kuma kwamishinan shari’a, Haruna Dederi, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haruna Dedieri ya ɗora alhakin abin da ke faruwa a jihar a kan wasu maƙiyan jihar waɗanda suke son ganin sun kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Kwamishinan ya musanta cewa gwamnatin jihar ta tauye haƙƙin ɗan Adam na Aminu Ado Bayero, wanda ta sauke daga kan sarauta, inda ya ƙara cewa lauyoyin gwamnati na duba hukuncin da nufin ɗaukaka ƙara a kai.
Haruna Dederi ya kuma koka kan yadda ƴan sanda ke ci gaba da karɓar umarni daga sama duk da cewa gwamnan shi ne babban jami’in tsaro na jihar.
Ya ƙara da yin kira ga ƴan Najeriya masu kishin ƙasa da abokan arziki daga ƙasashen duniya da su shiga tsakani domin a samu zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a jihar.
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya taya shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar bukukuwan Sallah.
Sarkin ya kuma sanar da cewa an dakatar da gudanar da hawa da aka shirya tun da farko biyo bayan shawarwarin da jami’an tsaro suka bayar domin a ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.
Asali: Legit.ng