'Yan Sanda Sun Cafke Mutum 2 Masu Safarar Makamai Ga 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da yin safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Mansir ya ce jami’an ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargin ne a ranar 4, ga watan Afrilu bayan samun sahihan bayanan sirri, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana sunayen waɗanda ake zargin a matsayin Alkali Danladi mai shekara 45 da Gayya Koddi mai shekara 40.
Hassan ya ce hukumar ta daɗe tana bibiyar Danladi bisa zargin safarar makamai ga ƴan bindiga, inda daga ƙarshe aka kama shi a ƙauyen Tsurutawa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Jos.
Ya ƙara da cewa an kama Danladi da ɗauke da wasu haramtattun bindigogi, rahoton jaridar Thisday ya tabbatar.
Hassan ya ce bincike ya kai ga kama Koddi, yayin da ake neman wasu mutum biyu da ake zargi.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Ana zargin Danladi ne da hannu wajen ba ƴan bindiga makamai ba bisa ƙa’ida ba. An kama shi ne a lokacin da ya fito daga Jos, jihar Filato.
"A lokacin da aka ritsa shi, an gano Danladi ya ɓoye wasu haramtattun bindigogi da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, bindigu guda biyar da ƙananan bindigogi guda biyu."
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke wasu ƴan bindiga mutum biyu a jihar.
Jami'an rundunar ƴan sandan sun cafke ƴan bindigan ne lokacin da suka yi yunƙurin kai hari a ƙauyen Madachi, cikin ƙaramar hukumar Sabuwa.
Asali: Legit.ng