Nnamdi Kanu: Obasanjo Ya Bayyana Abin da Ya Tattauna da Gwamnonin Kudu a Bayan Labule
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Enugu - Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ƙaryata cewa ya gana da gwamnonin kudu maso gabas ne kan sake Nnamdi Kanu.
Olusegun Obasanjo ya ce gwamnonin sun gayyace shi ne domin tattaunawa kan wasu abubuwa na musamman.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai taimakawa Obasanjo kan harkokin sadarwa, Kehinde Akinyemi ne ya yi karin haske kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kehinde Akinyemi ya ce tattaunawar Olusegun Obasanjo da gwamnonin ta fuskanci yadda za a inganta yankin kudu maso gabas ne.
Hadimin ya ce sai bayan sun gama tattaunawa da Obasanjo sannan gwamnonin suka yi magana kan neman sake Nnamdi Kanu.
Bayan Obasanjo da Emeka Anyaoku sun gama tattaunawa gwamnonin yankin sai gwamnonin suka saka labule.
Kuma a karshen tattaunawar sun yanke cewa za su tunkari shugaba Bola Tinubu domin ganin an saki Nnamdi Kanu.
Obasanjo ya ce gwamnonin sun gayyace shi tare da Cif Emeka Anyaoku domin tattaunawa kan matsalolin tsaro a yankin.
Ya kara da cewa sun kuma tattaunawa kan yadda za a haɓaka tattalin arziki yankin da samar da hadin kai, rahoton Vanguard.
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda ya ceci Cif Olusegun Obasanjo daga hannun yan fursuna yayin da aka kullesu a gidan yari.
Shehu Sani ya bayyana cewa an kulle shi tare da Obasanjo a gidan yari a lokacin mulkin Janar Sani Abacha inda yan fursuna suka so lakaɗawa Obasanjo duka.
Asali: Legit.ng