Home Back

Aminu Vs Sanusi II: Kotu Ta Shirya Raba Gardama, Za Ta Sanar da Halastaccen Sarkin Kano

legit.ng 2024/7/5
  • Yayin da ake ci gaba da rigimar sarauta, kotu ta shirya yanke hukunci kan sabuwar dokar masarautar Kano
  • Mai Shari'a Liman na babbar kotun tarayya ya sa ranar 20 ga watan Yuni domin yanke hukunci kan halascin mayar da Sarki Sanusi II
  • Wannan na zuwa ne bayan alkalin ya amince cewa kotun tana da hurumin sauraron ƙorafin Mai Martaba Sarki Aminu Bayero

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta shirya yanke hukunci jan sahihancin mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarautar Kano.

Kotun ta zaɓi ranar 20 ga watan Yuni, 2024 domin yanke hukunci kan halascin sabuwar dokar masarautar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi.

Sanusi II da Aminu Ado.
Kotu za ta yanke hukunci a karar da aka nemi soke sabuwar dokar nasarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Imran Muhammad Asali: Twitter

Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, shi ne ya sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar da lauyan Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗanagundi ya shigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan Ɗanagundi Chikaosolu Ojukwu ya shigar da sabon ƙorafi gaban kotun, inda ya nemi ta haramta amfani da sabuwar dokar masarautar Kani, The Nation ta ruwaito.

Ma'ana lauyan na neman kotu ta tabbatar da Mai Martaba Sarki Aminu Adi Bayero a matsayin halastaccen Sarkin Kano, kana ta dawo da sauran sarakuna hudu.

Tun farko dai kotun ta shure buƙatar lauyan shugaban majalisar dokokin Kano da majalisar ita kanta, Eyitayo Fatogun, SAN, waɓda ya nemi a rufe kundin shari'ar gaba ɗaya.

Fatogun ta ja hankali tare da ƙoƙarin gamsar da mai girma mai shari'a kan bukatar, inda ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin da kotun ta yi ranar Alhamis.

A ranar Alhamis da ta gabata kotun ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙorafin Ɗanagundi tun da ya shafa take haƙƙin Sarki Aminu.

Har ila yau Fatogun ya sanar da kotun cewa ya shigar da ƙara gaban kotun ɗaukaka ƙara, ya nemi alkali ya dakatar da yanke hukunci sai kotun gaba ta sanar da matsayarta.

Lauyan Antoni Janar da gwamnatin jihar Kano ya goyi bayan waɗandan ƙorafi da bukatun da Fatogun ya gabatar.

Mai shari'a Liman ya yanke cewa daga takardar da waɗanda ake ƙara suka gabatar masa, har yanzun ba a sa ranar shari'ar ba kuma babu shaidar sun ɗaukaka ƙarar.

Asali: Legit.ng

People are also reading