Aminu Vs Sanusi II: Kotu Ta Shirya Raba Gardama, Za Ta Sanar da Halastaccen Sarkin Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta shirya yanke hukunci jan sahihancin mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarautar Kano.
Kotun ta zaɓi ranar 20 ga watan Yuni, 2024 domin yanke hukunci kan halascin sabuwar dokar masarautar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi.
Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, shi ne ya sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar da lauyan Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Ɗanagundi ya shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan Ɗanagundi Chikaosolu Ojukwu ya shigar da sabon ƙorafi gaban kotun, inda ya nemi ta haramta amfani da sabuwar dokar masarautar Kani, The Nation ta ruwaito.
Ma'ana lauyan na neman kotu ta tabbatar da Mai Martaba Sarki Aminu Adi Bayero a matsayin halastaccen Sarkin Kano, kana ta dawo da sauran sarakuna hudu.
Tun farko dai kotun ta shure buƙatar lauyan shugaban majalisar dokokin Kano da majalisar ita kanta, Eyitayo Fatogun, SAN, waɓda ya nemi a rufe kundin shari'ar gaba ɗaya.
Fatogun ta ja hankali tare da ƙoƙarin gamsar da mai girma mai shari'a kan bukatar, inda ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin da kotun ta yi ranar Alhamis.
A ranar Alhamis da ta gabata kotun ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙorafin Ɗanagundi tun da ya shafa take haƙƙin Sarki Aminu.
Har ila yau Fatogun ya sanar da kotun cewa ya shigar da ƙara gaban kotun ɗaukaka ƙara, ya nemi alkali ya dakatar da yanke hukunci sai kotun gaba ta sanar da matsayarta.
Lauyan Antoni Janar da gwamnatin jihar Kano ya goyi bayan waɗandan ƙorafi da bukatun da Fatogun ya gabatar.
Mai shari'a Liman ya yanke cewa daga takardar da waɗanda ake ƙara suka gabatar masa, har yanzun ba a sa ranar shari'ar ba kuma babu shaidar sun ɗaukaka ƙarar.
Asali: Legit.ng