Home Back

Hukumar KNUPDA, ta rubuta jan fentin dakatar da ginin benen da ya ruguzo yau a Kano

dalafmkano.com 3 days ago

Biyo bayan da rushewar hawa na uku a wani bene da ake ginawa a unguwar Saharaɗa kwanar kasuwa da ke karamar hukumar Birni, yanzu haka hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA, ta rubuta jan fentin dakatar da aikin.

Magina da kuma makotan ginin benen dai da dama ne suka tsallake rijiya da baya, a lokacin da hawa na uku, na benen ya ruguzo a yau Alhamis.

A lokacin da wakilin gidan rediyon Dala FM, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki, ya halarci wajen da ginin ya ruguje ya ganewa idon sa jan fentin dakatarwar da hukumar KNUPDA, ta yi mai ɗauke da kwanan watan wannan rana ta 27 ga watan yunin 2024.

Ya kuma zanta da wani makocin wurin da shima ya kasance daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya, bayan da ginin ya ruguzo, inda ya ce suna zaune suka ji wata ƙara wanda hawa na uku na benen ya ruguzo amma ginin bai danne kowa ba.

Akan al’amarin ne wakilin namu ya so jin ta bakin guda daga cikin jagororin aikin ginin a lokacin da al’amarin benen ya ruguje amma sai dai yaƙi cewa komai.

Ya kuma tuntuɓi jami’ar hulda da jama’a ta hukumar tsara burane ta jihar Kano KNUPDA,
Bahijjah Mallam Kabara, ta wayar tarho, sai dai ta a bata lokaci za ta bincika, amma kawo yanzu bata kira ba domin yin ƙarin bayani akai.

People are also reading