Home Back

Yadda Wike Ya Kafa Tirihin Gudanar Da Ayyukan Ci Gaba A Abuja

leadership.ng 2024/7/1
Yadda Wike Ya Kafa Tirihin Gudanar Da Ayyukan Ci Gaba A Abuja

Ayyukan ci gaba da aka samar a cikin shekara daya a Abuja, babban birin tarayya, a karkashin shugabancin ministan, Nyesom Wike hakan ya yi matukar janyo hankalin Shugaban kasa, Bola Tinubu da kuma mazauna birnin wajen jinjina wa Wike.

Babu wata tantama, tauraruwar Wike ta haska a idon gwamnatin Tinubu a cikin shekara daya da ta gabata.

Bisa wannan ayyukan na ci gaba da Wike ya samar a Abuja, za a iya cewa tamkar ya dora ne kan irin ayyuakn ci gaba da ya samar a lokacin da yake kan karagar mulkin Jihar Ribas, inda ya yi wa’adin mulkinsa na tsawon shekaru takwas wanda har aka yi masa lakabi da sarkin aiki.

A nan za a iya cewa, nada Wike da Tinubu ya yi a matsayin ministan ya sanya shi farin ciki saboda ayyukan ci gaba da ya samar a Abuja, wanda da a ce, Tinubu ya biye wa surutun mutane na kiraye-kirayen da sukai ta faman yi na ganin cewa ba a nada Wike a mukamin minista, da yanzu irin wannnan ayyukan na ci gaba ba za a samu a Abuja ba.

Shi kan shi Tinubu ya tabbatar da cewa, wasu suka ba shi shawara kar ya nada Wike a wani mukami a cikin gwamnatinsa.

Tinubu ya tabbatar da hakan ne a lokacin kammadar da aikin titin ‘Arterial’ da ke a cikin Abuja wadda aka kashe naira miliyan 20, kuma sauya sunan titin zuwa Wole Soyinka Way.

Tinubu ya ce, “Mai girma minista na zo wajen kaddamar da aikin ne domin na gode maka kai da tawagarka, musamman bisa samar da cin nasara ga gwamnatinmu a cikin shekara daya. Ayyukan da ka gudanar a birnin Abuja sun sa mutane sun ji dadi sosai.

“Zuciyarta na cike da farin ciki da kuma alfahari da kai, domin sun yi tunanin cewa Wike ba zai iya yin wani aikin a zo a gani a matsayin minista ba, sai kuma gashi ba ka bai wa mara da kunya ba. Ayyuakan da kake kirkiro da su a birnin Abuja abun yaba wa ne.

Wike daga jam’iyyar PDP ya fito, wanda kuma ya karbi ajandar shirin Tinubu na magance kalubalen tattalin arziki, rashin tsaro da kuma samar da aikin yi tun lokacin kaddamar da yakin neman zaben 2023, da ake kira a turance, ‘Renewed Hope Agenda’.

Bugu da kari, bisa ayyukan ci gaba da Wike ya kirkiro da su a birnin a cikin shekara daya, wadanda kuma ana ganin su a zahari, hakan ya sanya an samar da sauye-sauyin na ci gaba a birnin a fannoni da dama.

Kazalika, a tarihin birnin ba a taba shafe kwanuka tara cur ana kaddamar da wasu ayyuka da aka yi a birinin ba, sai a lokacin mulkin gwamnatin Tinubu, inda shugaban ya kaddamar da ayyuka daban-daban da aka kirkiro da su a karkashin jagorancin Wike.

Ayyuakann sun hada da, kara kaddamar da aikin safarar jirgin kasa da zai yi zirga-zirga a cikin garin Abuja mai daukar fasinjoji kyauta har tsawon watanni bakwai da aikin gina titin ‘Southern Parkway, S8/S9; da na Christian Centre zuwa titin Ring Road 1; da titin B6, B12, da na Circle da aikin gadar Wuye da gidan mataimakin shugaban kasa da suka lashe kudi har naira biliyan 98.8.

A cewar Wike, kaddamar da wadannan ayyukan, sun nuna a zahairi gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen inganta harkokin kasuwanci da kuma inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

A lokacin sake kaddamar da aikin jirgin kasan, Wike ya ayyana yin jigilar matafiya kyauta har na tsawon wata biyu, wanda saboda jin dadin wannan ayyanawar ta Wike, sai Tinubu ya kara fadada jigikar zuwa watan Disamba domin a nuna jin kan gwamnatinsa take da shi ga ‘yan Nijeriya a fannin zirga-zirga.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, hukumar kula da raya birnin Abuja ce ta bayar da kwangilar aikin zirga-zirgar jiragen kasa a cikin birnin a 2007, inda aka fara gudanar da aikin gwaji na aikin daga watan Satumban 2018, inda aka kammala aikin a watan Maris na 2020.

Sai dai aikin zirga-zirgar jirgin ya samu koma baya sakamakon bullar annobar Korona da sace wasu manyan kayan aikin wanda hakan ya janyo aikin ya tsaya cak tun a 2020.

A yayin kaddamar da ayyukan titunan Southern Parkway, S8/S9 da na Christian Centre zuwa titin Ring 1, Tinubu ya ce, kammala ayyukan sun nuna zahirin manufar gwamnatinsa da gaske take don samar da ayyukan ci gaba.

Tinubu ya kaddamar da ayyukan da aka kashe naira biliyan 98.8 na aikin hanyoyin B6, B12 da na Circle da ke birnin, ya ce za su kara bunkasa kasuwanci da kuma inganta raruwar ‘yan Nijeriya.

A cewar Tinubu, zai iya bugun kirji da cewa ya kaddamar da ayyukan hanyoyi B6, B12 da na Circle a tsakiyar birnin Abuja a karkashin kulawar Wike. Ya ce wannan ayyukan tamkar zakaran gwajin dafi ne ga mulkinsa.

Aikin gadar Wuye da za ta sada sauran gundumomin da birnin na daga cikin manyan ayyukan ci gaba da Wike ya samar, domin sama da shekaru 20 da suka gabata ba a yi hakan ba.

Tinubu ya jinjina wa Wike bisa sadaukar da kai na cimma muradun ajandar shugabancinsa da ake kira a turance, ‘ Renewed Hope Agenda’, musamman bisa yadda a zahiri ajandar ta inganta rayuwar mazauna birnin.

A makon da ya gabata ne, aka kammala kaddamar ayyukan a cikin kwana tara, inda Tinubu ya sauya wa babban titin M18 da ke a yankin Guzape Lot II a Abuja, zuwa sunan Chinua Achebe.

Wike ya yi alkawarin kammala ayyukan da ke a yankin jakadu da ke a birnin tare da kuma bai wa Tinubu tabbacin kammala ayyukan a shekara mai zuwa.

Tun a farko, Wike ya kaddamar da ayyukan manyan hanyoyi tare da giggina makarantu a yankuna shida na birnin wadanda idan an kammala su, za a kaddamar da su.

People are also reading