Home Back

Ra’ayoyin Kasashen Duniya Game Da Harin Da Iran Ta Kaddamar A Kan Isra’ila

leadership.ng 2024/5/12
Ra’ayoyin Kasashen Duniya Game Da Harin Da Iran Ta Kaddamar A Kan Isra’ila 

Duniya ta kira taron gaggawa domin nazari a kan hare-haren da Iran ta kai wa Isra’ila na ramuwar gayya, yayin da kasashen duniya ke bayyana damuwa dangane da barazanar barkewar yaki a tsakanin kasashen biyu.

Sakatare Janar na majalisar, Antonio Guterres, ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana damuwa dangane da barazanar tabarbarewar al’amura a yankin gabas ta tsakiya.

Shugabar gudanarwar kungiyar kasashen Turai, Ursula von der Leyen ta bukaci Iran da ta gaggauta tsagaita wuta da kuma kiran kasashen da su tsagaita wuta tare da aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya.

Sakatare Janar na kungiyar kawancen tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce sun yi Allah-wadai da abin da ya kira matakin na Iran, yayin da suke ci gaba da sanya ido a kan abin da ke faruwa.

Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya bayyana harin na Iran a matsayin na rashin hankali, wanda ke iya fadada tashin hankalin da ke gudana a gabas ta tsakiya.

Firaministan Canada Justin Trudeau ya soki harin na Iran, inda ya sake jaddada goyan bayan kasarsa ga Isra’ila.

Ita kuwa China ta bayyana harin na Iran a matsayin fadadar rikicin Gaza, inda ta bukaci aiwatar da kudirin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya domin tabbatar da tsagaita wuta da kuma kawo karshen rikicin.

China ta bukaci kasashen duniya musamman masu karfin fada a ji domin ganin sun taka rawar ganin wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya.

Kasar Masar ta bayyana matukar damuwa da tashin hankalin tare da bukatar taka-tsan-tsan domin kaucewa fadawa yaki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah-wadai da harin Iran a kan Isra’ila, wanda ya bayyana shi a matsayin abin da ka iya jefa daukacin yankin cikin tashin hankali.

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya bayyana harin na Iran a matsayin rashin hankali.

Ita kuwa Rasha ta bayyana damuwa da harin, tare da samun taka-tsan-tsan, kamar yadda Qatar ta bukaci manyan kasashen duniya daukar matakin kwantar da hankalin bangarorin.

Kasar Saudi Arabiya ta yi kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa domin kare yankin gabas ta tsakiya.

Shugaban Amurka, Joe Biden, ya bayyana goyon bayansa ga Isra’ila bayan ganawa da manyan jami’an tsaron kasar, yayin da ya ce za su ci gaba da tallafa wa kasar.

Sauran kasashen da suka bayyana matsayi dangane da harin sun hada da Ukraine da Turkiya da Italiya da kuma Spain.

People are also reading