Gina gadar naira biliyan 27 a Kano, tsohon kwamishinan Ganduje ya ragargaji Abba Yusuf
Tsohon kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Kano, Muaz Magaji, ya caccaki gwamna Abba Yusuf kan fara aikin gina sabbin gadoji biyu a babban birnin jihar kan kudi naira biliyan 27.
Magaji wanda ya yi aiki a karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana ayyukan a matsayin abin da ba shi ake buka ta yanzu a Kano ba.
Idan ba a manta ba tun a ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Yusuf ya aza harsashin ginin daya daga cikin gadar sama a Kofar Dan’agundi da ke cikin birnin Kano, kan kudi Naira biliyan 15. Ya ce ginin zai inganta zirga-zirgar ababen hawa a tsohon birnin, a cewar sanarwar da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature ya fitar.
Gwamna Abba ya ce zai mayar da garin kano birni irin na zamani da za a rika alfahari da shi.
Sai dai kuma idan ba a manta ba a ba tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwakso, wanda shi ne ubangidan gwamna Yusuf, a watan Maris din shekarar 2021 ya nuna adawa da gina sabbin gadar sama a jihar, yana mai bayyana hakan a matsayin ba abi da Kanawa ke bukata ba ke nan a wannan lokaci.
Sai dai kuma ba kamar tsohon gwamna Ganduje ba da bashi ya rankatako wa jihar kano a lokacin ya gini gadar sama a shataletalen Hotoro, gwamna Abba na yanzu ya ce kudin kananan hukumomi ne zai rika zaftare wa ya narkawa a g