Home Back

Shugaba Tinubu Ya Fusata, Ya Ba da Sabon Umarni Kan Kisan da Aka Yiwa Sojoji a Abia

legit.ng 2024/11/4
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da kisan da aka yiwa jami'an tsaro na sojoji yayin da suke bakin aiki a jihar Abia
  • Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su tabbatar sun cafƙe masu hannu a wajen aikata wannan ɗanyen aikin kan sojojin
  • Shugaban ƙasan ya kuma gargaɗi ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) cewa gwamnati ba za ta zuba ido tana kallonsu suna aikata laifim cin amanar ƙasa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya gargaɗi ƙungiyoyin ƴan ta’adda da ke kai wa sojoji hari, yana mai cewa Najeriya na da karfin da za ta iya magance su.

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan kisan da aka yiwa sojoji a jihar Abia.

Shugaba Tinubu ya fusata kan kisan sojoji a Abia
Shugaba Tinubu ya umarci jami'an tsaro su cafko masu hannu a kisan sojoji a Abia Hoto: @DOlusegun Asali: Facebook

Me Tinubu ya ce kan kisan sojojin?

Shugaban ƙasan ya nuna takaicin cewa kisan ya faru ne watanni biyu bayan harin da aka kaiwa sojoji a Okuama da ke jihar Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya gargaɗi ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) da ke bikin ranar Biafra a lokacin da aka kai harin, cewa gwamnatinsa ba za ta zauna ta zuba ido tana kallo suna aikata laifin cin amanar ƙasa ba, cewar rahoton Daily Trust.

Wane umarni Tinubu ya ba da?

Shugaba Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su kamo masu shirya kashe-kashen da kuma masu kiran a zauna a gida.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace a lokacin da ake salwantar rayukan jami’an tsaronta, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

“Ina kira ga jami’an tsaro da ba kawai su kamo masu shiryawa da kai harin Aba ba, har ma da masu kiran mutane su zauna a gida. Aikinsu ba komai ba ne face laifin cin amanar ƙasa."
"Muna ƙoƙari wajen gina al'umma mai zaman lafiya da lumana amma kada wanda ya yaudari kansa cewa gwamnati ba zata ɗauki matakin da ya dace ba idan aka hallaka jami'an tsaronta."

- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Matawalle ya fusata kan kisan sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi magana kan kisan da aka yi wa sojoji yayin da suke a bakin aiki a jihar Abia.

Ƙaramin ministan tsaron ya bayyana cewa za a cafke masu hannu wajen aikata wannan mummunan ɗanyen aikin.

Asali: Legit.ng