Home Back

Barazanar Da Rashin Katabus Na Kananan Hukumomi Ke Yi Ga Dimokuradiyyar Nijeriya

leadership.ng 2 days ago
Barazanar Da Rashin Katabus Na Kananan Hukumomi Ke Yi Ga Dimokuradiyyar Nijeriya

Rushewar shugabanci da tsari a matakin kananan hukumomi babbar barazana ce ga dimokuradiyyar Nijeriya, wanda ke janyo alamun tambayoyi a wurin masana shari’a da kungiyoyin al’umma game da tabbacin dimokuradiyyar Nijeriya.

Rikicin siyasar da ke gudana tsakanin Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da wani bangaren majalisar dokokin jihar kan wa’adin shugabannin kananan hukumomi, ya fallasa yadda kusan dukkanin jihohin suka shiga ruguza tsarin shugabancin kananan hukumomi, inda zaben kananan hukumomi ya dogara da yadda gwamnoni suke so maimakon bin tsarin doka.

A zantawarsu da Jaridar LEADERSHIP, kwararru a fannin tsaro sun goyi bayan wani furucin da babban hafsan sojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya yi a baya-bayan nan na cewa rashin tsaro da ake fama da shi a yawancin sassan kasar nan, usamman arewacin Nijeriya na da nasaba da rashin gudanar da mulki yadda ya kamata a kananan hukumomi.

Masu ruwa da tsaki da suka zanta da LEADERSHIP sun bayyana cewa cin hanci da rashawa da mamaye siyasa a matsayin babban abin da ke kara tunzura gwamnonin yin watsi da kundin tsarin mulkin kasar, sannan sun ce hukuncin kotun koli zai kawo karshen danniyar da gwamnoni suke yi wa kudaden kananan hukumomi.

A halin da ake ciki a yanzu, akwai makudan nairori na kananan hukumomi.

Tsakanin Janairu zuwa Mayu 2024, dukkan matakan gwamnati uku sun raba naira tiriliyan 5.759 daga asusun tarayya. Kananan Hukumomi 774 sun samu naira tiriliyan 1.416 kan wannan adadi.

LEADERSHIP ta yi kiyasin cewa kananan hukumomi 774 za su iya samun kudaden da suka kai naira tiriliyan 3.39 a 2024.

A watan Janairun 2024, kananan hukumomin sun samu naira biliyan 288.928, sun kuma samu naira biliyan 278.041 a watan Fabrairu, naira biliyan 267.153 a watan Maris, naira biliyan 288.688 a watan Afrilu da kuma naira biliyan 293.816 a watan Mayu.

Bincike da ra’ayoyin masana da LEADERSHIP ta samo ya nuna cewa rashin bai wa kananan hukumomi ‘yanci na gurgunta mulkin dimokuradiyya da rura wutar rashin tsaro da haifar da cin hanci da rashawa da ta da zaune tsaye tsakanin gwamnatocin jihohi da sauran jama’a a bangare guda, sannan ana samun rudani a tsakanin gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya.

Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa kusan dukkanin gwamnonin jihohin da ke kan mulki sun nada mukaman rikon kwarya ta hanyar karya dokokin Nijeriya da kuma saba wa hukuncin kotun koli. Kamar gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya kai ga korar zababbun shugabannin kananan hukumomi.

Sai dai Jihar Anambra ta cire tuta wajen rashin bin doka kamar yadda wakilinmu ya ruwaito cewa an gudanar da zaben kananan hukumomi a shekarar 2014, shekaru goma da suka gabata.

A Jihar Ribas kuwa, an gudanar da muhawara kan wannan kuskure, inda wa’adin shugabannin kananan hukumomin da aka zaba ya kare a ranar 17 ga watan Yunin 2024.

Nan take gwamnan ya maye gurbinsu da masu rikon kwarya, yayin da majalisar jihar ta dage cewa ta tsawaita wa’adinsu ta hanyar wata doka mai cike da rudani.

Jihohin da suka gudanar da zaben kananan hukumomi a cikin shekaru uku da suka gabata sun hada da Sakkwato, Kaduna, Filato, Yobe, Ebonyi, Inugu, Kebbi, Neja, Adamawa, Oyo, Katsina, Ekiti, Borno, Gombe da Edo.

A watan Yulin 2021 ne Legas ta gudanar da zaben kananan hukumomi, amma ba ta shirin gudanar da wani zaben a 2025, wanda ya zarce shekaru uku da doka ta tanada.

A wasu jihohin kuma, an gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Kwara a shekarar 2017, an gudanar a 2018 a Jihar Imo, a watan Disamba 2020 an gudanar a Jihar Kogi, a watan Oktoba 2020 an yi a Akwa Ibom, a watan Mayu 2020 an gudanar a Jihar Kusu Ribas, a watan Yuni 2021 an yi a Jihar Jigawa.

Jihar Bauchi ta gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Oktoba na shekarar 2020. A Jihar Abiya ma an yi zaben a shekarar 2020, yayin da a Jihar Delta ya gudana a watan Maris na 2021.

Yayin da gwamnatin tarayya take kokarin dawo da tsarin mulki da cin gashin kai ga kananan hukumomi, wasu masa harkokin shari’a sun nuna rashin amincewa da tsarin.

Manyan lauyoyi da dama na Nijeriya sun yi ce-ce-ku-ce kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan jihohi 36 na tarayyar kasar na neman cin gashin kan kananan hukumomi 774 na kasar nan.

Babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, ya maka gwamnatocin jihohi a gaban kotun koli kan yadda gwamnonin jihohin ke rike kananan hukumomin ba bisa ka’ida ba.

Karar na neman cikakken ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnati a kasar nan.

People are also reading