Home Back

KUƊIN HAYA: Yadda wani mai gidan haya ya sheka lahira yayin musu da ɗan haya

premiumtimesng.com 2024/6/26
TURA TA KAI BANGO: Magidanci ya yi kukan-kura, ya kashe ɗan bindiga yayin ƙoƙarin hana garkuwa iyalin sa

Wani mai gidan haya mai suna Benjamin Apeh ya yanke jiki ya fadi yayin da yake musu da wani ɗan haya saboda ƙin biyan shi kuɗin haya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Omolola Odutola ya ce lamarin ya auku ne a kauyen Arigbabu dake karamar hukumar Sagamu.

Odutola ya ce rundunar ta samu labarin mutuwar Apeh bayan ‘yar sa Precious ta kawo ƙara ofishin ƴan sandan.

Ya ce Precious ta faɗi wa ƴan sanda cewa mahaifinta da ɗan hayan sun kwana su taf musu a tsakanin su saboda kuɗin haya da ɗan hayan bai biya ba.

Ɗan hayan mai suna Apeh ya yi barazanar kashe mai gidan hayan a duk lokacin da suka bɓarke da gaddama.

“Precious ta ce mahaifinta ya yanke jiki ya faɗi bayan sun takaddamar da tashiga tsakanin shi da ɗan hayan yaki ƙarewa.

Odutola ya ce rundunar ta fara farautar dan hayan domin kuwa bayan ya tabbata maigidansa ya mutu sai ya tattara ya arce.

People are also reading