Home Back

Kotu ta Garkame Mijin da ya Lakadawa Matarsa na Jaki a Kano

legit.ng 2024/7/1
  • Wani magidanci a jihar Kano, Abdullahi Muhammad ya gamu da fushin kotu bayan an shigar da kara ana tuhumarsa da yi wa mai dakinsa mugun duka har ta ji raunuka iri-iri
  • Tun da fari matar ta kai kokenra ofishin ‘yan sanda a karamar hukumar Gwale ta na neman a bi mata hakkinta bayan mai gidanta ya yi mata dukan kawo wuka
  • Abdullahi Muhammad ya musanta zargin da ake masa, inda lauyansa Umar I Umar ya nemi kotu ta bayar da belinsa, amma mai shari’a Ustaz Abadullahi Halliru ya ki amincewa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a filin hockey a jihar Kano ta fusata tare da tura wani magidanci gidan gyaran hali da tarbiyya bayan an zarge shi da dukan matarsa.

Ana zargin Abdullahi Muhammad da mantawa da so da kauna inda ya lakadawa matarsa dukan kawo wuka har ta kai ga danganawa da kotu.

Kano map
Kotu ta aike da mijin da ake zargi da dukan matarsa fursun Hoto: Legit.ng Asali: Original

Daily Trust ta wallafa cewa matar da ta sha dukan ce ta nufi ofishinsu tare da shigar da kara ta na so a bi mata hakkinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi ya musanta dukan matarsa

Tun da fari, wata mata ta garzaya ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Gwale ta na korafin mijinta ya yi mata dukan tsiya har da rauni.

Daga nan ne ‘yan sandan su ka mika lamarin kotu, inda aka fara zaman shari’ar domin jin yadda aka haihu a ragaya, kamar yadda jaridar aminiya ta wallafa.

Wanda ake zargi, Abdullahi Muhammad ya musanta cewa ya daki matarsa, a nan ne kuma lauyansa Umar I Umar ya nemi a bayar da belinsa.

Lauyan matar, barista Dandago ya roki kotu ka da ta bayar da belin wanda ake kara, kuma ya yi nasara domin mai shari’a Ustaz Abdullahi Halliru ya yi umarnin a mika shi fursun.

Mai shari’ar ya sanya ranar 14 Yuni, 2024 domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Kotu ta wanke Doguwa daga zargin kisa

A baya mun ruwaito muku cewa wata kotu a Kano ta wanke dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa daga tuhumar da gwamnatin jihar ke yi na kashe wasu jama'a yayin zaben 2023.

Kotu ta yi watsi da shari'ar saboda abin da ta kira rashin hujjoji tare da umartar gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta biya Doguwa diyyar Naira Miliyan 25 na bata masa lokaci.

Asali: Legit.ng

People are also reading