Home Back

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Ceto Mutane A Katsina Da Filato

leadership.ng 2024/5/20
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2

Dakarun sojin Nijeriya, sun kashe wasu ‘yan ta’adda a Katsina tare da ceto wasu mutane biyu da aka sace a Jihar Filato. 

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X, ta ce wata tawagar ‘yansanda da sojoji a jihar Katsina, sun kawar da ‘yan ta’adda a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Sanarwar ta ce yayin wani kazamin artabu, dakarun sun kawar da wani dan ta’adda guda tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu, harsasai da kuma babur.

Sojojin sun kuma gano wata jakar da ke dauke da tarin harsasai da abubuwan fashewa.

Dakarun sun kuma ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Maraban-Jema’a da ke karamar hukumar Jos ta Kudu ta Jihar Filato.

Sanarwar ta kara da cewa yayin da ‘yan bindigar suka hangi sojoji sai suka tsere suka bar wata mota kirar Peugeot 307 da wasu mutane biyu.

Sanarwar ta ce, “Mutane biyun da aka kubutar; Mista Abdul Bello da kuma wata Sekyen Melody Yapshak an mika su asibiti domin duba lafiyarsu,” in ji sanarwar.

People are also reading