Home Back

Zargin Satar N432bn: El Rufai Ya Ɗauki Matakin Shari’a Kan Majalisar Dokokin Kaduna

legit.ng 2024/7/5
  • Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya dauki matakin shari'a kan majalisar dokokin jihar
  • Malam El-Rufai ya garzaya kotu ne a ranar Laraba inda ya nemi a rusa rahoton majalisar da ya ce gwamnatinsa ta karkatar da N432bn
  • Tsohon gwamnan, wanda ya shigar da karar a kan tauye hakki ya ce majalisar Kaduna ba ta bashi damar kare kansa daga zarge zargen ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu kan zarginsa da ta yi da karkatar da N432bn a shekaru takwas na mulkinsa da kuma barin dimbin bashi.

A ranar Larabar nan ne El-Rufai ya shigar da kara kan take 'yanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda yake ƙarar majalisar Kaduna.

El-Rufai ya dauki matakin doka kan majalisar dokokin Kaduna
El-Rufai ya yi ƙarar majalisar dokokin Kaduna kan rahoton da ta fitar. Hoto: @elrufai Asali: Facebook

El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu

Rahoton Channels TV ya nuna lauyan tsohon gwamnan, Abdulhakeem SAN ne ta shigar da karar idan yake ƙalubalantar matakin majalisar na tuhumar El-Rufai da laifin 'zamba.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin takardar kararz El-Rufai ya nemi kotun da ta rusa wannan rahoto na majalisar dokokin sakamakon ba a bashi damar kare kansa kan zarge zargen da ake yi masa ba.

Baya ga majalisar dokokin Kaduna, El-Rufai ya haɗa da Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar a cikin wadanda yake kara.

Asali: Legit.ng

People are also reading