Zargin Satar N432bn: El Rufai Ya Ɗauki Matakin Shari’a Kan Majalisar Dokokin Kaduna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu kan zarginsa da ta yi da karkatar da N432bn a shekaru takwas na mulkinsa da kuma barin dimbin bashi.
A ranar Larabar nan ne El-Rufai ya shigar da kara kan take 'yanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda yake ƙarar majalisar Kaduna.
Rahoton Channels TV ya nuna lauyan tsohon gwamnan, Abdulhakeem SAN ne ta shigar da karar idan yake ƙalubalantar matakin majalisar na tuhumar El-Rufai da laifin 'zamba.'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin takardar kararz El-Rufai ya nemi kotun da ta rusa wannan rahoto na majalisar dokokin sakamakon ba a bashi damar kare kansa kan zarge zargen da ake yi masa ba.
Baya ga majalisar dokokin Kaduna, El-Rufai ya haɗa da Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar a cikin wadanda yake kara.
Asali: Legit.ng