Home Back

Peter Obi Ya Fadi Abu 1 da Ba Zai Daina Yi Ba a Najeriya

legit.ng 2024/6/18
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) ya yi Allah wadai da kisan da aka yiwa jami'an ƴan sanda a jihar Zamfara
  • Peter Obi wanda ya ce ba zai daina magana kan matsalar rashin tsaro a ƙasar nan ba ya koka kan yadda ƴan ta'adda ke kashe mutane
  • Ya buƙaci gwamnati da ta tabbatar ta cafko waɗanda suka aikata wannnan ɗanyen aikin tare da hukunta su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya yi Allah wadai da kisan da aka yiwa wasu jami'an ƴan sanda a jihar Zamfara.

An kashe jami'an ƴan sandan ne a wani hari da aka kai a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Peter Obi ya yi Allah wadai da kisan 'yan sanda a jihar Zamfara
Peter Obi ya koka kan matsalar rashin tsaro a Najeriya Hoto: Mr. Peter Obi Asali: UGC

Mutum 12, da suka haɗa da jami’an ƴan sanda bakwai aka kashe a yammacin ranar Laraba lokacin da ƴan bindiga suka kai hari a ƙauyen Magarya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammad Dalijan kwamishinan ƴan sandan Zamfara ya ce sama da ƴan ta’adda 300 ne suka kai harin.

Da yake mayar da martani a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, Peter Obi ya ce dole ne ya ci gaba da yin magana kan ɗumbin ƙalubalen tsaro da ke fuskantar Najeriya.

Ya kuma bayyana damuwarsa kan hare-haren da aka kai a jihohin Katsina da Neja.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra, ya ce hare-haren sun hana ƙasar nan samun ci gaba ta hanyar jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

"Dole ne domin ci gaban ƙasar mu, na ci gaba da yin magana kan ƙaruwar matsalar rashin tsaro a Najeriya."
"Matsalar rashin tsaro ta daƙile ƴancin mutanenmu na samum zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa mai ƴancin dimokuraɗiyya. Dimokuraɗiyyar da ake yin ta cikin fargaba, shirita ce."
"Iyalai na shiga halin baƙin ciki saboda kisan ƴan uwansu da ƴan ta'adda ke yi. Abin takaici matsalar tsaro na ci gaba da yaɗuwa a kowane ɓangare na ƙasar nan.
"Dole ne mu dakatar da kashe-kashen da ake yi a ƙasar nan. Rayuwar kowane ɗan Najeriya na da muhimmanci kuma dole a kare ta."

- Peter Obi

Peter Obi ya kuma yi kira ga gwamnati da ta zaƙulo waɗanda suka kai hare-haren tare da tabbatar da cewa an hukunta su.

Asali: Legit.ng

People are also reading