Home Back

Alhajin Jigawa Ya Tsinci Jaka Ɗauke da Makuɗan Kuɗi, Ya Miƙawa NAHCON

legit.ng 2024/7/5
  • Wani mahajjaci daga jihar Jigawa a Arewacin Najeriya ya nuna kyakkyawan hali yayin da ya tsinci jakar hannu ɗauke da maƙudan kudi a Madinah
  • Alhaji Abba Saadu Limawa ya yi cigiya domin bai wa jakar kayansa amma ba a samu ma ita ba, don haka ya kai wa hukumar NAHCON
  • Shugaban hukumar alhazai ta jihar Jigawa,.Ahmad Umar Labo ya ce tsintuwar ta biyo ta hannunsa kafin a miƙawa shugaban NAHCON a taron kammala Arafah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Wani Alhaji daga jihar Jigawa ya mayar da jakar hannu da ya tsinta a Masallacin Annabi SAW da ke Madina a ƙasar Saudiyya.

Dun da jakar na ɗauke eda Dalar Amurka 800, kimanin N1,185,000 a kudin Najeeiya, Alhajin ya mayar da ita ga hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa NAHCON a Makkah.

Alhazai a filin Arafah.
Alhaji daga Jigawa ya mayar da jakar da ya tsinta a Madinah Hoto: Inside The Haramain Asali: Facebook

Alhajin mai suna, Abba Saadu Limawa ya fito ne daga kauyen Limaw aa ƙaramar hukumar Dutse ta jihar Jigawa, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya mayar da jakar domin a yi cigiya ga shugaban NAHCON na ƙasa, Malam Jalal Ahmad Arabi a wurin taron da aka shirya bayan kammala tsayuwar Arafah a Makkah.

Ahmad Umar Labo, shugaban hukumar jin daɗin alhazai na Jigawa ya tabbatar da wannan hali nagari da alhajin ya nuna a wata sanarwa.

Ya ce Alhaji Abba Saadu ya yi cigiyar jakar na tsawon kwanaki biyu a Masallacin Anmabi SAW amma ba a samu mai ita ba.

Ahmad ya ƙara cewa bayan rashin samun mai jakar, mutum ya tuntuɓi shugabansu na Jigawa wanda shi kuma ya sanar da hukumar NAHCON.

Daga ƙarshe dai Alhajin ya bai wa hukumar jakar ɗauke da kuɗafen da ƴa tsinta ba tare da ya taɓa ko kwandala domin a ci gaba da cigiya.

Abubuwan da huɗubar Arafah ta kunsa

A wani rahoton na daban miliyoyin mahajjata daga ƙasashen daban-daban suka gabatar suka yi tsayuwar Arafa a kasa mai tsarki a lokacin hajjin bana.

Hawan Arafa yana daya daga cikin manyan ayyukan Hajji da ake bukatar mahajjata maza da mata sa gudanar yayin aikin Hajji.

Asali: Legit.ng

People are also reading