Home Back

Kuncin Rayuwa: Jan Hankali Ga Iyaye Da Yayyen ‘Yan Mata

leadership.ng 2024/5/4
Kuncin Rayuwa: Jan Hankali Ga Iyaye Da Yayyen ‘Yan Mata

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.

Muna rokon Allah ya ba mu alhairan da ke cikin wannan wata mai girma na Ramadana.

Jan hankalin da zan yi tare da tunatarwa a yau, a kan iyaye maza da mata da kuma su kansu ‘ya’ya ne, sannan da kuma yayye wadanda ke kasancewa a matsayin magadan uba, da kuma wadanda ke da kanne mata.

Hakika mun shiga wani irin yanayi na kuncin rayuwa, wanda iyaye ba lallai ba ne su iya yi wa ‘ya’yansu abubuwan da suke bukata ba, musamman a bangaren da ya shafi dinkunan sallah da sauran makamantansu.

Don haka, yana da matukar muhimmanci iyaye su sa ido a kan ‘ya’yansu, su kuma kula sosai wajen ganin da me da me yarinya ta shigo gida da me kuma ta fita? Ka da ‘yarka ko ‘yarki ko kanwarka ta rika shigowa gida da kayayyakin dinki da sunan saurayi ne ya ba ta ta kuma karba, ba tare da kun yi bincike ba, har sai wani abu ya je ya zo; sannan a fara neman mafitar da za ta yi wuyar samu.

Ba don komai na ce haka ba, sai don sanin yadda dabi’un wasu mazan take a halin yanzu, wasu ba su da kirki ko kadan; domin kuwa za su iya amfani da halin da ake ciki na kuncin rayuwa a kan atamfa kadai ko shadda ko takalmi ko wani abu da yarinya za ta saka da sallah, su lalata mata rayuwa.

Don haka, dole ne a mayar da hankali kwarai da gaske a kansu, sannan duk abin da ta kawo; ya kamata a san wanda ya bayar a kuma ji dalilin bayarwar. Kazalika, idan abin aka ga ya yi yawa ma sai a bincika a dalili, tunda ita ba ‘yar sarki ba ce; iyakar abin da Allah ya hore iyaye a yi hakuri da shi, sannan kuma ku ja wa ‘ya’yanku kunne, saboda yanzu ‘yan mata suna da irin wannan hangen, yarinya za ta ga waya a hannun wata; sai ta saka abin a ranta cewa; ya kamata ita ma ta rike irin ta da sallah, ko da kuwa ta halin kaka ne.

Haka nan, idan ta ga kaya ko jallabiya ko riga ko wani abu dai makamancin irin wannan a hannun kawayenta, ita ma sai ta ce lallai sai ta samu, kar ka yarda a matsayinka na uba ko a matsayinki na uwa, idan an kawo irin wannan ki yi shuru, ya kamata ki binciki asalin abin da yake faruwa.

Kazalika, kai ma da kake a matsayin babban wa na dawo gare ka, lallai ne ka sa ido a kan kannanka sosai, ba zai yiwu don lokacin azumi ne saurayi ya zo ya kai karfe daya ko karfe sha biyu yana tare da kanwarka ba, haka nan yau wannan ya zo, gobe wannan ya zo.

Sannan, yau wannan ya kawo takalmi; gobe wancan ya kawo shadda, jibi kuma wancan ya kawo doguwar riga, dole ne ku sa ido a mayar da hankali ka da a ga cewa ai ana cikin halin ha’ula’i, ko ana cikin wani irin yanayi da iyaye ba za su iya yi wa ‘ya’ya dinkunan da suke so ba, duk abin da Allah ya yassare sai a yi hakuri a karba, ya kamata kuma a lura da cewa; duk abin da ka same shi ta wata hanya ta daban, idan da ka yi hakuri ta hanyar halak ma zai zo ya same ka har inda kake.

Don haka, yanzu lokaci ne na addu’a da ya kamata su kansu samari da ‘yan matan su yi amfani da shi a roki Allah subhanahu wata’ala ya kawo mana sauki da sassauci, idan budurwa ce ki roki Allah ya kawo miki miji nagari, haka nan saurayi shi ma ya roki Allah ya kawo masa mata ta gari.

A takaice, wannan shi ne jan hankalina da fatan Allah ya sa za mu sa ido yadda ya kamata, Allah ya sa mu dace, amin.

People are also reading