Home Back

Gawa Ta Ƙi Rami: Tsohuwar da Likita Ya Ce Ta Mutu Ta Buɗe Ido Ana Shirin Jana’izarta

legit.ng 2024/7/2
  • Wani abin al'ajabi ya faru a yankin Nebraska da ke ƙasar Amurka, inda wata dattijuwa ta farfaɗo a na shirin gudanar da jana'izarta
  • Likitoci ne suka tabbatar da mutuwar matar a wani gidan kuka da dattawa inda aka garzaya da ita gidan da za a yi jana'izarta amma ta farka
  • Sai dai hukumomi sun ce likitoci a wani asibiti sun sake tabbatar da mutuwar dattijuwar karo na biyu bayan farfaɗowarta, amma ana bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nebraska, Amurka - Hukumomi sun ce wata dattijuwa 'yar Nebraska da aka ayyana ta mutu a gidan kula da tsofaffi ta farfaɗo a lokacin da ake shirin jana'izarta.

Mataimakin babban shugaban ofishin 'yan sandan Lancaster, Ben Houchin ya ce an garzaya da dattijuwar mai suna Constance Glantz zuwa asibiti bayan da ta farka.

Tsohuwar da ta farfado ana shirin jana'izarta a Amurka
Amurka: Dattijuwa ta farfado ana shirin jana'izarta bayan likita ya ayyana ta mutu. Hoto: Getty Images Asali: Getty Images

Kafar labaran CNN ta ce Ms. Glantz mai shekaru 74 a duniya wacce ke zaune a Lincoln Neb., ta sake mutuwa awanni bayan farfaɗowarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattijuwa ta farfado ana shirin jana'izarta

Constance Glantz na samun kulawa daga gidan rainon dattawa na The Mulberry da ke a Waverly lokacin da aka ayyana cewa ta mutu a ranar Litinin.

Akalla bayan awanni biyu da kai Ms. Glantz gidan jana'iza na Butherus-Maser & Love da ke Lincoln aka ga ta bude ido, in ji rahoton New York Times.

Ben Houchin ya ce:

"A halin yanzu babu wata alama da ta nuna gidan kula da dattawan sun aika ta'addanci, amma muna kan yin bincike."

Ms. Glantz ta mutu a karo na biyu

Mataimakin shugaban 'yan sandan ya ce ma'aikacin da ke shirya jana'izar matar ya yi saurin kiran 911 bayan ganin ta na numfashi, kafar labaran NBC.

Wata ma'aikaciya a hukumar kashe gobara da aikin ceto, M.J. Lierman ta ce an garzaya da Ms. Glantz zuwa wani asibiti inda likitoci suka ayyana ta mutu karo na biyu.

Ben Houchin ya ce har yanzu ba a gano musabbabin mutuwar matar ba amma za a gudanar da binciken gawa a safiyar Talata.

Matar aure ta farfado ana shirin kona ta

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa wata mata mai suna Bujji Aamma 'yar Indiya ta bude ido ana dab da kona ta bayan da aka yi tunanin ta mutu.

Dakin kona gawar sun ce ana samun irin wannan abun saboda mutanen garin ba sa bukatar shaidar mutuwa kafin kona gawar dan uwan su.

Asali: Legit.ng

People are also reading