Home Back

Ana Fargabar Dawowar Dogayen Layin Fetur, Bashin Mai Ya Taru a Kan NNPCL

legit.ng 2024/10/4
  • Akwai yiwuwar a samu bullar dogayen layin neman man fetur a kasar nan yayin da bashi ke kara taruwa kan kamfanin fetur na kasa NNPC
  • An gano cewa yanzu haka ana bin kamfanin bashi mai dimbin yawa da ya kai Dala Biliyan 6 wanda haka zai jawo raguwar shigo da fetur cikin kasar
  • Yanzu haka masu shigo da man fetur guda biyu sun dakata da shigo da mai Najeriya har sai an fara biyansu bashin kudin da su ke bin kamfanin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- An shiga fargabar dawowar matsalar man fetur Najeriya bayan an gano kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya fada matsalar bashi.

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka kamfanin NNPCL ya gaza biyan masu bashi man fetur kudinsu da ya kai $6bn.

Pius Utomi Ekpei
Bashi ya yiwa kamfanin NNPCL katutu, an daina ba shi bashin fetur Hoto: Pius Utomi Ekpei Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa NNPCL ya kasa biyan kudin cikin kwanaki 90 kamar yadda ya ke cikin sharadin cinikkayar fetur din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu ba Najeriya fetur sun dakata

Rahotanni sun gano cewa ana bin kamfanin NNPCL bashin $4bn-$5bn a watan Janairu yayin da kamfanonin da ke bawa kasar nan fetur su ka ragu.

Business Day ta wallafa cewa akalla kamfanoni biyi ne su ka dakata da bawa kasar fetur har sai an biya su kudadensu da suka makale a NNPCL.

Tarin bashin da ake bin kamfanin ya sa an samu raguwar kamfanonin da su ka bawa Najeriya fetur a watannin Yuni da Yuli.

Zuwa yanzu har an fara samun bullar layukan man fetur a Abuja da Legas saboda karancinsa da ake fama da shi.

NNPCL ya bude gidajen CNG

A wani labarin kun ji cewa ana fatan samun saukin farashin man fetur, yayin da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bude gidajen sayar da isakar gas na CNG guda 12 a jihar Legas da Abuja.

Ministan albarkatun man fetur, Ekperikpe Ekpo ne ya kaddamar da gidajen inda ake ganin za su taimaka wajen rage matsalar dumamar yanayi da kuma rage dogaro da man fetur.

Asali: Legit.ng

People are also reading