Ana Fargabar Dawowar Dogayen Layin Fetur, Bashin Mai Ya Taru a Kan NNPCL
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- An shiga fargabar dawowar matsalar man fetur Najeriya bayan an gano kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya fada matsalar bashi.
Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka kamfanin NNPCL ya gaza biyan masu bashi man fetur kudinsu da ya kai $6bn.
Daily Trust ta wallafa cewa NNPCL ya kasa biyan kudin cikin kwanaki 90 kamar yadda ya ke cikin sharadin cinikkayar fetur din.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun gano cewa ana bin kamfanin NNPCL bashin $4bn-$5bn a watan Janairu yayin da kamfanonin da ke bawa kasar nan fetur su ka ragu.
Business Day ta wallafa cewa akalla kamfanoni biyi ne su ka dakata da bawa kasar fetur har sai an biya su kudadensu da suka makale a NNPCL.
Tarin bashin da ake bin kamfanin ya sa an samu raguwar kamfanonin da su ka bawa Najeriya fetur a watannin Yuni da Yuli.
Zuwa yanzu har an fara samun bullar layukan man fetur a Abuja da Legas saboda karancinsa da ake fama da shi.
A wani labarin kun ji cewa ana fatan samun saukin farashin man fetur, yayin da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bude gidajen sayar da isakar gas na CNG guda 12 a jihar Legas da Abuja.
Ministan albarkatun man fetur, Ekperikpe Ekpo ne ya kaddamar da gidajen inda ake ganin za su taimaka wajen rage matsalar dumamar yanayi da kuma rage dogaro da man fetur.
Asali: Legit.ng