Home Back

ARAFAT: Za a kwallara rana mai zafin gaske, mahajjata a yi takatsantsan – Gargaɗin Likitoci

premiumtimesng.com 2024/7/7
ARAFAT: Za a kwallara rana mai zafin gaske, mahajjata a yi takatsantsan – Gargaɗin Likitoci

A daidai mahajjata na cigaba da kinkintsawa domin nausa wa Muna tun daga daren Alhamis, mahukunta da likitoci a kasar Saudiya na cigaba da yi wa alhazai gargaɗin su yi taka tsantsan da kawunan su saboda za a kwallara ranar gaske a ranar Arafa wanda za a yi tsayuwar ranar Asabar.

Mahukunta sun shaida cewa za a kwallara rana da zai kai kusan maki 72 cikin 100 na ma’aunin yanayi a wasu wurare a filin.

Dalilin haka ya sa ake ta yin kira ga Alhazai da su bi a hankali tare da a yawaita shan ruwa a koda yaushe da kuma kada a takura wa kai a lokacin aiki.

Ranar Asabar da safe ne za a ɗunguma Mzuwa filin Arafat da ga Muna.

Bayin Allah kusan mutum miliyan biyu ne daga kasashen duniya za su halarci wannan tsayuwa a wannan rana.

Tuni har an fara garzayawa da Ƴan Najeriya zuwa Muna domin a rage cinkoso da kuma a samu damar kimtsawa domin aikin na bana.

People are also reading