“Ban San da Zamanku Ba”, Fubara Ya Yi Kakkausar Suka Kan ’Yan Majalisar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Siminialayi Fubara, gwamnan Rivers, ya ce wanzuwar ‘yan majalisar dokokin jihar ya ta'allaka ne ga amincewarsa ko akasin hakan.
Jaridar The Cable ta ruwaito Fubara ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin karbar bakuncin shugabannin siyasa da na gargajiya daga jihar a gidan gwamnati.
Fubara yana dagawa 'yan majalisar kafa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Rivers ya ce babu mambobi a majalisar jihar, yana mai cewa ya yanke shawarar "daga masu kafa" saboda yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar.
Fubara ya ce ya amince da yarjejeniyar zaman lafiya ne bisa fahimtar cewa akwai alaka tsakaninsa da ‘yan majalisar dokokin jihar, rahoton Channels TV.
Gwamnan Rivers ya ce ya kawar da kai a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar duk da karfin da yake da shi, inda ya ce dayan bangaren bai nuna hakan ba.
Ya koka da cewa a kullum magoya bayansa na fuskantar barazana da kai hare-hare a jihar.
"Wadancan rukunin mutanen da ke da'awar cewa 'yan majalisarmu ne ba 'yan majalisa ba ne, a wajena ba su wanzu ba.
"Ni ne nan na kyale su har suke jin kansu sun isa akan komai, sai dai da zan ga dama yanzu, da na wofantar da su gaba daya."
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito jagoran 'yan adawa a Najeriya, Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu da Kashim Shettima suka bar Najeriya lokaci daya.
Atiku ya wanda ya yi tambayar "wa ke jogarantar Najeriya a yanzu?" ya yi magana ne yayin da Shettima ya shirya zuwa Amurka alhalin Tinubu bai dawo kasar ba tun bayan zuwansa Saudiya.
Sai dai rahotanni daga baya sun bayyana ce Shettima ya fasa zuwa Amurka sakamakon matsalar jirgin sama da aka samu.
Asali: Legit.ng