Home Back

Ana Fargabar Mutane da Yawa Sun Mutu Yayin da Jirgin Sojoji Ya Jefa Bam a Filin Idi a Jihar Arewa

legit.ng 2024/5/20

Jihar Zamfara - Ana fargabar an kashe mutane da dama a kauyen Kukawa da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, yayin da sojojin suka kai farmaki ta sama.

Wani dan kauyen, Musa Abubakar wanda ya sha da kyar ya shaidawa jaridar Punch ranar Juma’a cewa suna cikin Sallar Idi ranar Laraba kwatsam sojojin sama suka yi ruwan bama-bamai a yankin.

Jirgin yakin sojoji.
Rundunar soji ta musanta kashe fararen hula a Zamfara Hoto: Nigeria Air Force Asali: Facebook

Abubakar ya ce harin bama-baman sojojin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 40 a ranar Ƙaramar Sallah.

"Muna cikin sallar idi kawai muka hango jirgin yaƙin sojoji ya tunkaɗo wurin. Jirgin na ƙarisowa kwatsam muka ji kara mai ƙarfi, nan take kowa ya yi takansa.
"Ina daga cikin waɗanda suka taki sa'a suka tsira lafiya amma mutane da yawa sun mutu, wasu kuma sun samu raunuka. Na rasa mutane 13 a dangina," in ji shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jirgin sojojin ya saki ruwan bama-baman ne bayan wasu yan bindiga sun buɗe masa wuta.

Ya ce:

"Jirgin ya zo zai wuce ta ƙauyen kwatsam ƴan bindigar duka fara harbinsa, hakan ya sa sojoji suka jefa bama-bamai a kauyen ana tsaka da sallar idi, kuma mutane da yawa sun mutu."

Da yake zantawa da jaridar ta wayar tarho, kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Laftanar Suleiman Omale, ya ce sojoji na yakar ‘yan bindiga ne ba fararen hula ba.

Ya kara da cewa ba shi da masaniyar am kashe wasu fararen hula da ba ruwansu yayin luguden wutar ta sama.

"Muna yakar ‘yan fashin daji ne, ba ‘yan Najeriya marasa laifi ba. Ba ni da masaniyar wani farar hula da aka kashe a yayin farmakin.”

Asali: Legit.ng

People are also reading