Home Back

Jamus ta yi nasara karo na biyu a wasan Turai

dw.com 2024/7/7
EM 2024 | Jamus lokaci wasan neman cin kofin kasashen Turai
Jamus lokaci wasa da Hangari

Jamus ta kasance kasar farko da ta  haye mataki na gaba tun bayan da aka fara gasar Euro 2024 sakamakon lashe daukacin wasanninta da ta yi cikin sauki da araha. Ko da shi ke dai a wasanta na biyu ba ta yi ruwan kwallaye kamar lokacin da ta kara da Scotland ci 5-1, amma Mannschaft ta doke Hangari da ci 2-0. Hasali ma, 'yan wasanta da take ji da su Gündogan da Jamal Musiala ne suka fi ba da gudunmawa wajen lallasa kasar Hangari. Ko da kwallon farko, kyaftin din tawagar Jamus Ilkay Gundogan ne ya mika wa Musiala kwallon da ya ci ana minti na 22 da fara wasa. Yayin da dan wasan tsakiya na kungiyar FC Barcelona ya ci kwallo na biyu a minti na 67 da fara wasan bisa gudunmawar dan wasan baya na kungiyar Stuttgart Maximilian Mittelstädt.

Sai dai tsaron gidan Jamus Manuel Neuer na ganin cewa abokan wasansa sun nuna hadin kai duk da matsin lamba da suka sha daga Hangari:

"Tabbas nuba ganin cewar kungiyar ta kankama, tana tattar da ruhin hadin kai. Kowa na bakin ciki idan ba mu taka leda sosai ba, amma kuma muna farin ciki sosai idan muka samu nasara. Har wani mataki za mu yi kaiwa? wannan abu ne mai wuyan hasashe saboda komai na iya faruwa a irin wannan gasar. Idan muka ci-gaba, za mu ci karo da manyam kungiyoyi, amma yanzu ya yi wuri wajen bayyna abin da zai faru."

Ya zuwa yanzu dai, kwallon daya tilo aka yi nasarar zuwa wa mai tsaron gidan Jamus Manuel Neuer, duk da hare-hare da ya sha daga tawagar Hangari. A hakika nin gaskiya ma dai, Hangari ba ta da tabbacin hayewa zagaye na gaba, saboda Switzerland ta doke su da ci 3-1 a wasan farko, yayin da Jamus ta samu nasara a kanta da 2-0. Sai da ma dan wasanta Roland Sallai ya kai ga kai mummunan farmaki a farko-farkon wasan kafin Manuel Neuer ya yi kawar da harin.

Dama dai filin wasa na Stuttgart ya cika makil da magoya bayan Jamus, lamarin da ke bai wa 'yan wasan koci Julian Nagelsmann kwarin gwiwa na kai wa matakin kusa da na karshe kamar lokacin da kasra ta dauki bakuncin kofin duniya na kwallon kafa a shekarar 2006.  Shi ma dan wasan tsakiya da ke bugaw na Real Madrid Toni Kroos ya danganta abin da ke faruwa da Jumma'ar da za ta yi kyau wacce aka fara gane ta daga Laraba:

"Mun fara gasar da kafar dama, inda muka  buga wasan farko a lokacin da muke cike da kwarin gwiwa: kuma wannan shi ne abin da zai fi muhimmanci a zagaye na gaba da kuma sauran matakai, domin za a samu fitattun kungiyoyi  kuma zai fi sauki mu baras da wasa. Dole ne mu shawo kan matsalolinmu, kamar yadda aka saba, kwarin gwiwa na taimakawa sosai."

A ranar Lahadi ne Jamus za ta kara da Switzerland a wasan karshe na rukunin A, yayin da a daren jiya Switzerland ta yi kunnen doki da Scotland ci 1-1, lamarin da ya sa ta rasa damar farfadowa, yayin da Scotland take nesanta kanta daga jin kamshin zagaye na gaba na Euro 2024. Sai  'yan wasam Kuroshiya sun samu nasara a kan Italiya ciki kwanaki biyar masu zuwa ene kawai za su iya hayewa mataki na gaba saboda maki biyu ne gare su a halin yanzu.

People are also reading