Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya Saduda, Ya Nemi Ayi Sulhu da Gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja - Bayan shafe shekaru a tsare, shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya zubar da makaman yaki inda ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tattauna da wakilan gwamnati.
Nnamdi Kanu ya shaidawa kotun tarayya da ke zamanta a Abuja cewa ya shirya zaman yayin da aka ci gaba da shari’ar tuhume-tuhume kan ta’addanci da cin amanar kasa da ake masa.
Vanguard News ta tattaro lauyoyin Mista Kanu ne su ka bayyana matsayarsu karkashin jagoranicn Mista Alloy Ejimakor, inda ya ce sashe na 17 na dokar babbar kotun tarayya ya bayar da damar cimma masalaha ta tattaunawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran lauyoyin Nnamdi Kanu, Alloy Ejimakor, ya shaidawa kotu cewa sun nemi amfani da sashe na 17 na dokar babbar kotun tarayya ne domin fargabar za ta soke bukatunsu guda biyu.
Bukatarsu ta farko ita ce kotu ta garkame shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi bisa zargin karya umarnin kotu, kamar yadda TVC News ta wallafa.
Sai bukatarsu ta biyu na tuhumar kotun da cewa ba ta da hurumin sauraron shari’ar, kuma tuni lauyan gwamnati Adegboyega Awomolo ya yi martani.
Ya ce babban lauyan kasa ne kawai ya ke da ikon tattunawa kan zarge-zargen da su ka shafi cin amanar kasa da ta’addanci.
A baya mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu bayan lauyoyinsa sun bukaci haka.
Mai shari'a Binta Nyako ta kuma yi umarnin gaggauta ci gaba da shari'ar da ake yi tsakanin gwamnatin Najeriya da Mista Kanu kan zargin ta'addanci da cin amanar kasa.
Asali: Legit.ng