InnalilLahi: Duniyar Musulunci Ta Yi Rashi Bayan Rasuwar Babban Limamin Borno
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - An shiga jimami bayan rasuwar tsohon babban limamin jihar Borno da yammacin yau.
Marigayin Imam Asil ya rasu ne da yammacin yau Juma'a 7 ga watan Yuni a birnin Maiduguri da ke jihar.
Imam Asil ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya, kamar yadda rahoton Zagazola Makama ya tabbatar a shafin X.
Mutuwar babban limamin ga girgiza mutane da dama inda suka bayyana limamin a matsayin mutumin kirki.
Karin bayani na tafe....
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng