Home Back

InnalilLahi: Duniyar Musulunci Ta Yi Rashi Bayan Rasuwar Babban Limamin Borno

legit.ng 2024/7/3
  • Tsohon babban limamin jihar Borno, Imam Asil ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar jinya
  • Marigayin ya rasu ne da yammacin yau Juma'a 7 ga watan Yuni a birnin Maiduguri da ke jihar
  • Mutuwar limamin ya tayar da hankulan jama'a wanda aka kwatanta da mai hidima ga addinin Musulunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - An shiga jimami bayan rasuwar tsohon babban limamin jihar Borno da yammacin yau.

Marigayin Imam Asil ya rasu ne da yammacin yau Juma'a 7 ga watan Yuni a birnin Maiduguri da ke jihar.

Imam Asil ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya, kamar yadda rahoton Zagazola Makama ya tabbatar a shafin X.

Mutuwar babban limamin ga girgiza mutane da dama inda suka bayyana limamin a matsayin mutumin kirki.

Karin bayani na tafe....

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

People are also reading