Home Back

Yadda Aka Kaddamar Da Kungiyar Tafiyar Matasa A Abuja

leadership.ng 2024/8/23
Yadda Aka Kaddamar Da Kungiyar Tafiyar Matasa A Abuja

A ranar Asabar din da ta gabata ce, aka yi bikin kaddamar da kungiyar tafiyar matasa ta kasa reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, taron da ya samu halartar wasu daga cikin jiga-jigan kungiyar daga wasu sassa na jihohin Arewa.

Da yake gabatar da jawabi, shugaban kungiyar reshen Abuja Malam Ibrahim Muhammed Garki, ya gode wa Allah bisa ga basu damar kaddamar kungiyar cikin salama, ya kuma nuna jin dadinsa da ya zama shi ne farkon shigaban kungiyar, domin a cewarsa Abuja ta fita daba da kowacce jiha a Nijeriya a matsayinta na Babbar Birin Tarayya.

“Mun zavo matasa ne daga kowace shiyya ta nan buja domin haskawa duniya cewa a shirye muke akan wannan tafiya ta matsa, kuma Allah da ikonsa mun gaya musu kuma sun karba hannu biyu. Abu na farko dai hadin kai muke bukata daga matasannan, idan muka samu hadin kai to duk abin da muka a gaba za mu samu nasararsa. Abu na biyu mu wayar dasu su sani cewa, bangar siyasa ba ita ribar ba, mun yi a baya mun ga babu riba, sannan akwai abubuwa da dama da aka bar matsa a baya saboda mun cire hannunmu a harkar siyasa, abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata, mun koma shaye-shaye da abubuwa marasa kyau. Yana daga cikin abubuwan da mu son ganin kawo karshensu ga matasa,”in ji shi.

Ya kara da cewa ya kamata shugabanninmu su sani cewa mulki a yanzu sai da matasa, amma matasan nan da su ake amfani wajen satar mutane domin karbar kudin fansa, to wannan tafiya na burin ganin ta kawo kashen duk irin wadannan abubuwa.

Shima a na sa jawabin Shugaban Tafiyar Matasa Reshen Jihar Kano, kuma mai ba da shawara ta fuskra shari’a Nura Shehu Ido Dodon Voye, cewa ya yi, wannan tafiya ta kunshi abubuwa da suke damunmu kuma suke damun al’ummarmu musamman Arewa, inda aka bar mu a baya da abubuwa da dama, waxanda suka hana mu cimma burika da dama. Misalin rashin tsaro, rashin aikin yi da karancin ilimi, waxannan na daga cikin abubuwan da wannan Tafiya ta Matasa ke kokarin ganin ta ya kawo karshensu ta hanyar wayar da kan matasa da iznin Allah.

Taron ya samu halartar Abba Halliru Ashura, Shugaban Matasa na kasa, sai Jidda Sa’id Abubakar, Shugabar Kula da walwalara jama’a ta Kasa da Gudanarwa, , Nura Shehu Ido Dodon Boye, Chairman Tafiyar Matasa Reshen Jihar Kano kuma Mai Ba Da Shawara Na Kan Shari’a Na Kasa 02, Yunusa Adamu Sokoto Sakataren Tsare-tsare reshen Sokoto.

People are also reading