Home Back

Sin Na Dukufa Kan Kiyaye Mabambantan Halittu

leadership.ng 2024/9/28
Sin Na Dukufa Kan Kiyaye Mabambantan Halittu

A watan Yuni na shekarar 2023, mujallar ilmin halittu ta kungiyar masana na “Linnean” ta kasa da kasa, ta wallafa bayanin da Zhang Guoyi ya rubuta game da wani sabon nau’in dodon kodi da ya gano yayin da ya yi nazarin halittu a dutsen Fohui, wanda shi ne dalibin jami’ar koyar da ilmin malanta ta lardin Shandong. An rada wannan sabon nau’in dodon kodi da sunan “dodon kodi na Fohui na kasar Sin” bisa wurin da aka gano shi, abun da ya nuna cewa an amince nasarar gano wannan sabon nau’in halitta.

Yadda aka gano wannan sabon nau’in halitta, ba ya rabuwa da kokarin da Sin din ta dade tana yi wajen kiyaye muhalli da mabambantan halittu. Inda ta tsara kundin dokokin kiyaye muhallin halittu, tare da samar da tsarin dokokin kare muhalli da mabanbantan halittu na “1+4+N”, kana ta kafa tsarin jan-layi na kiyaye halittu, wanda ya kasance irinsa na farko a duniya, matakin da ya kiyaye filayen kasar da ya zarce kashi 30%.  Ban da wannan kuma, kasar Sin ta gaggauta gabatar da tsarin ware filayen kare muhalli dogaro da kafa gandun daji na kasa, tare kuma da ci gaba da ingiza aikin nazarta mabambantan halittu da aikin sa ido da kimantawa. Bisa alkaluman da aka bayar, wadannan manufofi sun ba da kariya ga kashi 90% na nau’o’in tsare-tsaren muhallin halittun kasa, da kashi 74% na nau’o’in halittun dabbobin daji, da tsirran daji da gwamnatin Sin ke mai da muhimmanci a kai.

Ban da wannan kuma, Sin tana kokarin zurfafa hadin gwiwa da kasashen duniya, don taka rawar gani wajen kiyaye mabambantan halittu a duniya. A matsayinta na kasar da ta karbi bakuncin gudanar da taron COP15, Sin ta ba da jagoranci wajen cimma tsarin kiyaye mabambantan halittu na Kunming-Montreal, kana shekaru a jere ne ta zama kasar da ta zuba jari mafi yawa a yarjejeniyar kare mabanbantan halittu, kana kasa mai tasowa da ta fi zuba jari a asusun kiyaye muhalli na duniya.

Ranar 22 ga wata, rana ce ta kiyaye mabambantan halittu, kuma Sin ta gabatar da bayanin jerin sunayen nau’o’in halittu da take da su na shekarar 2024, inda aka yi rajistar nau’o’in halittu 141,484, daga cikinsu akwai 6,423 da suka kasance sabbin nau’o’i da aka gano. Alkaluman da suka shaida nasarorin da aka samu wajen kiyaye muhallin halittu a kasar Sin, da ma kokarin da gwamnatin kasar take yi wajen kiyaye mabambantan halittu. (Mai zana da rubutu: MINA)

People are also reading